Taron wanda zai samu halartar wasu shugabannin siyasa da ‘yan kasuwa da wakilan kungiyoyin farar hula, na da nufin tara jari ga kasar ta Ukraine da ke fuskantar shekara ta hudu na yaki.
Taron na Roma, wanda shi ne irinsa na hudu, zai kuma tattauna batun shigar Ukraine cikin kungiyar EU.