Ina makomar tattalin arzikin kasashen AES?
May 27, 2025Sabon bankin na hadin gwiwa na zuba jari da raya tattalin arziki wanda kasashen na AES suka kaddamar tashin farko ya mallaki jarin da ya kai miliyan dubu 500 na CFA, kwatankwacin Euro 7,600.
Wannan banki na da burin samar wa kasashen na AES cikakken 'yanci a fannin harkokin tattalin arziki da kuma rage dogaro da kasashen yammacin duniya da ma kungiyoyin duniya da bankunan kasa da kasa, wajen samar da kudin saka jari da kuma aiwatar da ayyukan raya kasashen uku da inganta rayuwar al'ummominsu.
Tuni dai 'yan kasuwa a Jamhuriyar Nijar din suka fara bayyana gamsuwarsu da matakin kafa bankin na AES, tare ma da bayar da shawarwari. To sai dai Malam Siraji Issa shugaban Kungiyar kare hakin dan Adam ta Mojen, na ganin wannan batu na kafa bankin AES farfaganda ce kawai.
Bayan kaddamar da babban bankin na BCID-AES, kasashen sun ce za su hada kai wajen samar da jarinsa nan zuwa ranar 30 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2025, domin ba shi damar soma aiki gadan-gadan.