Kasar Togo ta dakatar da kafofin labaran Faransa
June 17, 2025Talla
Hukumar kula da kafofin watsa labarai ta kasar Togon ta ce gidajen labaran na Faransa suna watsa wasu shirye-shiryen da suka nuna son kai, wanda hakan ke kawo cikas ga zaman lafiya da kuma martabar kasar.
Wannan mataki ya biyo bayan zanga-zangar adawa da gwamnatin Togon wanda aka yi cikin ‘yan kwanakin nan, inda aka kama mutane da dama, ciki har da wasu ‘yan jarida.
Tashohin RFI da France 24 dai sun bayyana mamakin wannan hukunci da aka dauka ba tare da gargadi ba, suna mai jaddada biyayya ga ka'idojin aikin jarida na gaskiya da kuma daidaito.