Kasar Indiya ta dauki matakan diflomasiya a kan Pakistan
April 23, 2025Kasar Indiya ta sanar da dakatar da yarjejeniyar musayar ruwa da ke tsakaninta da Pakistan tun shekaru 65 da suka gabata, kwana guda bayan harin da aka kai kan fararen hula a yankin Kashmir. Wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Indiya, Vikram Misri, ya shaida wa manema labarai cewa, kasarsa ta rufe iyakarta ta kasa da Pakistan tare da rage jami'an diflomasiyya, har sai Pakistan ta yi watsi da goyon bayan ayyukan ta'addanci a kan iyakar kasashen biyu.
Sai dai a nata bangaren, Pakistan ta kira taron majalisar tsaron kasa a ranar Alhamis don mayar da martani ga sanarwar gwamnatin Indiya. Wannan hukumar dai ta kunshi manyan jami'an farar hula da na soji, tana haduwa ne kawai a lokutan da Pakistan ke cikin tsanani ko fuskantar barazana. Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin wannan harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 26. Sai Indiya na zargin Pakistan da aikata shi, duk da sanarwa da ta fitar don nuna "damuwa" da mika sakon "ta'aziyya" ga wadanda suka jikkata.