Karfafa hulda tsakanin Mali da Rasha
June 23, 2025Shugaban gwamnatin mulkin sojan Mali Janar Assimi Goita, wanda yake ziyarar aiki a kasar Rasha ya shaida wa Shugaba Vladimir Putin na Rasha cewa yana bukatar ganin karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Karin Bayani: Shugaban gwamnatin mulkin sojan Mali ya fara ziyara a Rasha
Janar Goita wanda ya dauki madafun iko ta hanyar zuwa mulki a kasar da ke yankin yammacin Afirka mai fama da matsalolin tsaro, inda ya raba gari da kasar Faransa wadda ta yi wa kasarsa mulkin mallaka. Har yanzu kasar ta Mali tana fama da tashe-tahsen hankula daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi.
Shugabannin kasashen na Rasha da Mali sun saka hannu kan yarjejeniyar bunkasa ciniki da habaka tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Ita dai Mali tana sahun gaba na kasashen da suke da ma'adinin zinare.