SiyasaGabas ta Tsakiya
Gaza: Karancin kayan abinci ga Falasdinawa
March 5, 2025Talla
Bayanin Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniyar na zuwa ne, biyo bayan matakin Isra'ila na hana kai kayan agaji yankin Zirin Gazan da suka hadar da abinci da man fetur da kuma magunguna. Isra'ilan dai ta ce ta yi haka ne domin tilasta Hamas ta amince da wani tsari na tsagaita wuta da kuma sakin 'yan kasarta da take garkuwa da su, sai dai kungiyoyin da ke rajin kare hakkin dan Adam na bayyana matakin Isra'ilanda kokarin amfani da yunwa a yaki. Mafi aksarin al'ummar Gaza dai sun dogara ne da kayan agaji, bayan kwashe watanni 16 ana gwabza yaki tsakanin Hamas da Isra'ila da ya dai-dai-ta yankin na Zirin Gaza baki daya.