Kananan yara na kara fadawa cikin tashin hankali
June 20, 2025Talla
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce rahoton shekara-shekara a kan yara cikin rikici ya nuna karuwar matsalolin da ke tayar da hankalin yara kanana da kashi 25 cikin 100.
Yankin Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Somaliya da kasashen Najeriya da Haiti su ne suka fi samun irin matsaloli na take hakkokin kananan yara.
A shekarar 2024, Antonio Guterres ya bayyana cewa yara ne suka fi fuskantar tasirin hare-hare a kai- a kai, tare da shan wahala daga rashin bin yarjejeniyoyin tsagaita wuta, da kuma tsanantar matsalolin jin kai.