Wasanni: Gasar Bundesliga da sauran wasanni
May 19, 2025Dan wasan Bayern Munich kuma kyaftin din Ingila Harry Kane ya lashe takalmin zinare na gasar Bundesliga, bayan da ya fi kowa zura kwallo a raga a kakar wasanni ta bana da kwallaye 26. Masu biye masa a matsayi na biyu su ne Patrick Schick na Bayer Leverkusen da Serhou Guirassy na Borussia Dortmund da kowa cikinsu ke da 21. Sai Jonathan Burkardt na Mainz mai 18 yana take musu baya.
Bayer Leverkusen da ke a matsayi na biyu da Eintracht Frankfurt da ke a matsayi na uku da kuma Borussia Dortmund da ta samu matsayi na hudu da kyar da jibin goshi, sun samu gurbin halartar gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai wato UEFA Champions League a kaka mai zuwa. Kungiyar Freiburg da matsayi na hudu ya kufce mata a raanar karshe ta koma mataki na biyar za ta shiga gasar Europa League, yayin da Mainz da ke matsayi na shida za ta buga wasan share fagen shiga gasar Conference League wato play-off.
Crystal Palace ta zama zakarar gasar kofin kalubale na Ingila na bana, bayan da ta samu nasarar doke Manchester City da ci daya mai ban haushi ta hannun dan wasanta Eberechi Eze. Wannan nasara, ta ba ta damar halartar gasar zakarun kungiyoyin Turai ta UEFA Europa mai zuwa. A gasar Premier League ta Ingila a wannan makon za a fafata a ranar Litinin tsakanin Brighton da Liverpool, yayin da a Talatar wannan makon, Crystal Palace za ta kece raini da Wolves kana a fafata tsakanin Manchester City da Bournemouth.
A karshen mako dai Arsenal ta karbi bakuncin Newcastle ta kuma lallasa ta da ci daya mai ban haushi ita ma Chelsea ta karbi bakuncin Manchester United ta kuma caskara ta da ci daya mai ban haushi yayin da Aston Villa ta lallasa Tottenham Hotspur da ci biyu da nema.
A wasan karshe na gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Afirka CAF Champions League, Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu za ta kara da Pyramids ta Masar a ranar 24 ga wannan wata na Mayu, sannan su buga zagaye na biyu a kasar Masar ranar daya ga watan Yuni mai kamawa. A zagayen farko na wasan karshe na CAF Confederations Cup Berkane ta Morocco ta samu nasara a kan Simba SC ta Tanzania da ci biyu da nema a Marocco, inda za su buga zagaye na biyu a Tanzania ranar 25 ga wannan wata na Mayu kafin sanin zakara a gasar.
A karon farko Afirka ta Kudu ta lashe gasar matasa 'yan kasa da shekaru 20, bayan samun nasara da ci daya mai ban haushi a kan Moroko. Morokon ta je wasan karshe ne bayan casa mai masaukin baki Masar, wadda ta fitar da Ghana. Ita ko Afirka ta Kudu Flying Eagles ta Najeriya ta doke. Najeriyar ce dai ta fi ko wace kasa lashe kofin, inda take da guda bakwai sai Ghana da Masar da suke da hurhudu. Afirka ta Kudu da Morocco da Najeriya da kuma Masar za su wakilci Afirka, a gasar 'yan kasa da shekaru 20 ta duniya da za a gudanar a kasar Chile a cikin watan Oktobar wannan shekara.
Lamba biyu a duniya a fagen kwallon Tennis Carlos Alcaraz na kasar Spain ya samu nasarar lashe gasar Italian Open ta bana da aka kammala ranar Lahadi, bayan casa lamba daya na duniya Jannik Sinner na kasar Italiya da ci 7-6 da 7-5 da 6-1. Wannan ne kuma ya kawo karshen nasarori 26 a jere da Sinner ya samu a wasannin da ya buga, ba tare da an doke shi ba.
Rabon da wani dan kasar Italiya ya lashe wannan gasa tun a shekara ta 1976 da Adriano Panatta ya daga kofin. A bangaren mata kuwa lamba 4 a duniya Jasmine Paolini 'yar Italiya ce ta lashe gasar ta bana, bayan lallasa lamba 2 ta duniya Coco Gauff ta Amurka da ci 6-4 da 6-2. Wannan ne karo na farko, a tsawon shekaru 40 da 'yar Italiya ta daga kofin Italian Open.
A bangaren gasar kwallon kwando ta Amurka kungiyar Oklahoma City Thunder ta samu nasarar zuwa zagayen karshe wato Conference finals bayan casa Denver Nuggets da maki 125-93 a karawar zagayen dab da na karshe, inda za ta tunkari Minnesota Timberwolves a wasan karshe wato Western Conference finals.
Yayin da ita kuma kungiyar Indiana Pacers, za ta barje gumi da New York Knicks a wasan karshe na Eastern Conference. Za a fara wasannin a ranar Laraba 21 ga wannan wata na Mayu, a kokarin neman lashe gasar kwallon kwandon Amurka NBA. Za dai a iya samun sabuwar kungiya da za ta zama zakara, a cikin shekaru 52 a tsakanin masu fafatawar.