Harajin Trump na firgita kamfanonin motocin Koriya da Japan
March 27, 2025Hukumomi a Koriya ta Kudu, sun bayyana anniyarsu ta kara daukar matakan kariya ga durkushewar masa'antun kera motoci na kasar, bayan shelar karin harajin shigo da motoci na kaso 25 cikin 100 da gwamnatin Dnald Trump ta Amurka ta yi ga wasu kamfanonin kasashen Asiya da dama.
Sabon harajin Amurka kan Canada da Mexico ya fara aiki
Tuni sanar da matakin ya fara shafuwar manyan kamfanoni irinsu Toyota na kasar Japan, inda hannayen jarin kamfanin ya yi kasa sosai a kasuwar hada-hadar hannun jari, kana kuma masana sun yi hasashen Koriya ta Kudu ma dai kamfanomninta za su tsinci kansu cikin tsaka mai wuya.
Trump ya lafta harajin kaso 25% ga karafa dake shiga Amurka
To amma sai dai gwamnatin Seoul ta bayyana anniyarta na daukar sabbin matakan da suka dace a farkon watan gobe da nufin rage wa matsalar harajin Dnald Trump kaifi. Fiye da kaso 15 ne kamfanonin kasashen biyu ke shigarwa na motocin da ake bukata a Amurka,