Kalubalen da Shugaba Oligui zai fuskanta a Gabon
April 14, 2025Oligui Nguema wanda, cike da shaukin murna da farin ciki, ya yi jawabi ga dimbin magoya baya da suka yi dandazo a ofishinsa na yakin neman zabe domin taya shi murna. Sai dai shugaban ya kara kira ga jama'a da su jira kotun tsarin mulki ta bayyana sakamako na dindindin, yana mai cewa wannan nasara ce ga 'yan kasar Gabon baki daya. A taron manema labarai da ya gudanar, ya ce: " Allah na tare da bayinsa, ba zai yi watsi da su ba. Babu yadda za a yi a ci gaba, sai an hada kai. Ya kamata mu manta da abubuwan da suka faru a baya. Zabe ya riga ya kare, akwai ayyuka da aka bude a kasarmu, ina kira a gare ku da ku mayar da hankali a kan aiki a wannan Jamhuriya ta biyar."
Karin bayani:Zaben shugaban kasa a Gabon bayan kawo karshen Bongo
Tun da farko, ministan cikin gida Hermann Immongault ya ce Oligui Nguema ya samu nasarar wa'adin mulki na shekaru bakwai da kuri'iu 575,200 ko kuma kashi 90.3% na kuri'iun da aka kada. Babban abokin hamaiyarsa Alain-Claude Billie ya samu kashi uku cikin dari na kuri'iun, yayin da sauran 'yan takara shida suka gaza samun ko da kashi daya cikin dari na kuri'iun da aka kada a zaben.
Kafar rediyon gwamnati ta yi riga Malam masallaci
Tun kafin a kammala kidaya kuri'iun ne kafar yada labaran gwamnatin Gabon ta sanar da cewa Oligui Nguema na kan gaba da tazara mai yawa. Masu kada kuri'a, a kasar mai yawan jama'a miliyan biyu da dubu dari uku sun yi fitar dango kwansu da kwarkwata domin kada kuri'a a zabe na farko na kawo karshen mulkin soja. Hasali ma, ministan cikin gida ya bayyana yawan jama'ar da suka fita kada kuri'ar da cewa sun kai kashi 70 .4 % na wadanda suka yi rejista.
Karin bayani: Yunkurin maido da tsarin mulki a Gabon
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ta wayar tarho ya taya Oligui Nguema murnar samun nasara da kuma gudanar da zabe a cewar sanarwa daga ofishin shugaban. Sannan, kwana guda bayan zaben titunan Libreville babban birnin kasar sun kasance shiru sabanin zabukan 2016 da 2023 inda aka samu tarzoma da tashin hankali.
Karin bayani:Gabon: Sojoji na shirya zaben raba gardama
Worah Jean Yves, wani mazaunin Libreville ya ce: "A da, ba ma iya fita waje saboda harbe-harben bindiga da balle kantuna domin kwasar ganima. Amma a wannan karon, komai ya tafi salin-alin ba tare da wasu matsaloli ba. Akwai ma 'yan kasashen waje da wasu 'yan uwa 'yan Gabon da suka zo daga wasu gundumomi."
Matsalolin da ke gaban Oligui Nguema a Gabon
Sabon shugaban farar hula na Gabon zai fuskanci tarin kalubale a kasar mai arzikin man fetur, kama daga lalacewar abubuwan more rayuwa zuwa talauci da ya zama ruwan dare da kuma dumbin bashin da ya yi wa kasar katutu. Carole Eyindo, wata yar kasar Gabon ta yi tsokaci tana mai cewa: "Abin da nake sa ido a nan gaba a kan sabon shugabar kasar, shi ne ya ci gaba da abin da ya fara. A cikin kasa da shekaru biyu ya yi abubuwa masu yawa. A saboda haka, muna so ya kara a kan haka kamar yadda ya yi alkawari, kuma mun san cewar ba zai yi karya ba."
Karin bayani:Sabon sharadin takarar shugaban kasa a Gabon
A karon farko, 'yan jaridun kasashen waje da 'yan jaridu masu zaman kansu na cikin gida sun samu damar daukar hoto wajen kidayar kuri'u. Masu sa ido na kasashen duniya da suka halarci rumfunan zabe a fadin kasar, ba su ga wani abu da ya kauce wa ka'ida ba kamar yadda rahotanni suka nunar.