kace-nace bayan da aka yi wa ASUU kishiya a Najeriya
October 5, 2022Yi wa wadannan kungiyoyin biyu da suka balle daga Asuu sabon rejista, mataki ne da ake yi wa kalon yunkurin na gwamnatin na karya lagon kungiyarar sakamakon ci gaba da jayayya da take yi da gwamnatin a kan batun yajin aikin.Tun a shekarar 2018 ne kungiyar CONUA take neman a yi mata rijista.
Ko me gwamnatin ke nufi da yi wa kungiyoyi biyu rijista a daidai lokacin da akea tsakiyar wannan rikici? Dr Chris Ngige da ke zama ministan kodago da ingantuwar aiki na Najeriyar ya ce: ‘' Duk wata tattaunawar da aka gayyaci kungiyar malaman jamioi ta Asuu, su ma za'a gayyace su, ba sauran maganar kungiya daya a batun malaman jamioi, a yanzu guda uku ne''.
Me ra'ayin dalibai da iyaye ?
Iyayen yara da daliban na cike da fatan ganin wannan dabarara da gwamnatin ta dauka za ta yin tasiri a kokarin shawo kan matsalar, kamar yadda Hajiya Binta Mu'azau, daya daga cikin iyayen yara ta yi nuna doki da shakku kan zuwan sabbin kungiyoyin malaman jami'o'i a kasar.
Tuni dai kungiyar malaman jami'oIin Najeriya ta Asuu ta mayar da murtani a kan kafa sabbin kungiyoyin biyu da suka zama kishiyoyi ga kungiyarsu. Sai dai ga Malam Bashir Baba da ke sharhi a kan al'ammuran yau da kullum ya bayyana fahimtarsa a kan tasirin wannan mataki da gwamnatin ta dauka. .
Ko wadannan sabbin kungiyoyi na da karfi na komawa don ci gaba da karatu a jamio'in, shine babban lamari. Ga dalibai da iyayensu abinda suka fi so su ji kuma su gani shi ne a kawo karshen yajin aikin, gwamnati da sauran kungiyoyi uku su ci gaba da dogon Turanci har su sulhunta.
Ita dai kungiyar Asuu tana ci gaba da neman gwamnatin tarayyar Najeriya ta biya mata jerin bukatunta kafin ta soke yajin aikin da ta shafe wata da watanni tana gudanarwa, lamarin da ya gurganta harkar karatu a jami'o'i mallakin gwamnati.