Jirgin ruwa ya kife da mutum 50 a Sokoton Najeriya
August 18, 2025Fiye da mutane 40 sun bace bayan da jirgin ruwa mai dauke da mutane 50 zuwa wata kasuwa a jihar Sokoto da ke Najeriya ya kife.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar NEMA ta ce hadarin ya faru ne ranar Lahadi a jihar ta arewa maso yammacin Najeriya a yayin da damuna ke kara nisa.
Mutum 13 sun mutu a hatsarin kwale kwale a Najeriya
Fasinjojin na kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Goronyo ce, wacce aka sani da fice wajen fitar da kayan amfanin gona a jihar.
Kawo yanzu an ceto mutane goma, in ji Zubaida Umar, shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA, a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X.
Hukumar ta ce tana hada kai da hukumomin yankin da masu bada agajin gaggawa wajen gudanar da aikin nema da kuma ceto wadanda suka bace.
Kwale-kwale dauke da mutane 200 ya kife a tsakiyar Najeriya
A makonni uku da suka gabata, akalla mutane 13 sun mutu kuma wasu da dama sun bace bayan wani jirgin ruwa dauke da kusan fasinjoji 100 ya kife a jihar Neja, a arewa ta tsakiya Najeriya.