Jirage sun dakatar da zuwa Isra'ila bayan wani hari
May 5, 2025Babban kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Jamus wato Lufthansa, ya dakatar da jigilarsa zuwa zuwa Isra'ila bayan harba makami mai linzami da mayakan Houthi na kasar Yemen suka yi zuwa Isra'ila. Makamin dai ya fadi ne a wajen filin jirgin sama na Ben Gurion da ke birnin Tel Aviv, kamar yadda rahotanni ke tabbatarwa.
Kamfanin na Lufthansa, wanda ke da wasu kamfanonin jiragen sama a cikinsa; da suka hada da na Swiss da na Austria da ma Brussels Airlines, ya ce dakatar da jigilar zuwa Isra'ila za ta kai ranar Talatar da ke tafe. Akwai ma karin wasu manyan kamfanonin jirage na duniya da suka sanar da dakatar da jigila zuwa Isra'ila saboda wannan hari.
Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da faruwar lamarin, kuma ta ce mutane takwas ma sun jikkata. Wannan ne dai karo na farko da mayakan tawayen Houthi na Yeman ke harba makami zuwa babban filin jigin sama da ke a Tel Aviv din.