Najeriya: Jawabin shugaba Buhari ya bar baya da kura
October 2, 2020Kalamn shugaban Najeriya sun harzuka wasu alummar kasar biyo bayan ya kwatanta farashin da ake sayar da kowace litar man fetur a wasu kasashe da duk da cewa suna da arzikin mai irin Najeriya amma suke sayar da mai da tsada. Shugaban ya bada misali da kasar Chadi da kowace litar mai take Naira 362 da Jamhuriyar Nijar N346 Saudiyya kuma kowace lita ana sayar da ta kan Naira 168 a Masar kuwa Naira 211, don haka babu basira man fetur ya yi arha a Najeriyar fiye da kasar Saudiyya. Kungiyoyin kwadagon Najeriyar na kan gaba wajen maida murtani kan wannan batun na shugaban kasar Najeriya, inda suka yi kakkausar suka kan yadda jawabin shugaban ya banbanta da zahiri.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace tattalin arzikin Najeriyar na fuskantar rashin samun kudin shiga da kaso 60 cikin 100, tare da bayyana cewa dole sai an tunkari zahirin matsalar sai dai shugaban ya ce"Babu wata gwamnatin da take yin abinda muke yi a yanzu da dan abinda muke da shi.’’ Sanar da sabon farashin man da shugaba Muhammadu Buhari yayi a wannan wata daga Naira151.56 a watan Satumba zuwa Naira 161 na nuna barin kasuwa ta yi halinta a kan farashin mai a Najeriya.