Shin gwarzo a zahiri ko a kafafen sada zumunta?
September 9, 2025Shekaru uku bayan da ya karbe iko da tsinin bundiga, Kyaftin Ibrahim Traoré na Burkina Faso na nuna kansa a matsayin wani sabon jagoran juyin juya hali. Ana wa matashin shugaban kasar kallon ja-gaba a shafukan sada zumunta, amma kuma a cikin gida kima da tagomashinsa na dada dusashewa, saboda takaita 'yanci da walwalar fadar albarkacin baki da 'yancin bani'Adama, kamar yadda kungiyoyin 'yan fafutikar kasa da kasa ke bayyanawa.
Juyin mulki:
A ranar 30 ga watan Satumban 2022, Shugaban gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ya kifar da gwamnati, juyin mulki ne a cikin wani juyin mulki, domin kuwa matashin sojan ya kawar da Paul-Henri Sandaogo Damiba ne da shi ma ya murde wuyan wata gwamnatin farar hula. Traore ya bayyana a madafan ikon ne bisa hujjar yakar masu ikrarin jihadi da suka yi wa kasar kaka gida, inda ma ya yi alkawarin kawo karshen masu ayyukan ta'addancin kasar a cikin tsukun watanni shida har ma a gudanar da zabe.
Sai dai a daura da hakan, Shugaba Traore ya karfafa madafan ikonsa ne, ya kuma sauya salon rundunar tsaro ya nada gwamnatin da ke yi masa biyayya sau da kafa ya kuma karya inda ba gaba tare da hana zakarun duk wasu masu adawa da gwamnatinsa cara, a cikin 'yan watanni shida Traore ya zama lasharika-lahu. Daga karshe dai Kyaftin Ibrahim Traoré ya bayyana cewa zabe ba shi ne a gaban gwamnatinsa ba. Sai dai kuma lamarin tsaro tun daga wannan lokaci zauke yanzu na kara ta'azzara ne a Burkian Faso. Koma dai Paul Melly, wani kusa a cibiyar bincike ta Chatham House ya bayyan acewa kaso kimanin 70% na fadin kasar a yanzu na rike ne a hannun masu ikrarin jihadi, to amma sai dai kuma shafukan sada zumunta da dama na 'yan baranda da farfaganda.
Sai dai ga dan Jarida Justin Yarga, dan asalin Burkian Fason da yanzu haka ke hijira a Swidin, na mai cewa sun tattauna da da 'yan kasar da dama, kuma sun gano sirri da ke tattare da wannan dabarar ta yi wa shugaban kasarsa Burkina Faso farfaganda.
Raba gari da Faransa:
Batun na raba gari da uwargijiyar kasarsa Faransa na gaba-gaba daga cikin jerin batutuwan da Kyaftin Ibrahim Traoré ke yawan furtawa a duk lokacin da damar hakan ta samu, kana matashin shugaban ya gina kimarsa da wadannan akidun, da caccakar tsarin tsofaffin shugabannin kasar da ya kira 'yan barandar Faransa da Turai da cin hanci ya musu katutu.
A baya bayan nan ne dai shugaba Traore ya kafa wata sabuwar dokar tsarin iyali da ke ci gaba da tayar da kura a bakunan kungoyoyin kasa da kasa masu kare hakin dan Adam, dokar da a ciki aka tanadi matakin zare wa kowane dan Burkina Faso takardar zama dan kasa muddin ya yi izgili ga gwamnatin da manufofinta.