Rikicin Najeriya ya dauki hankalin Jaridun Jamus
June 20, 2025Guguwar tashin hankali a Najeriya, an kashe mutane da dama a harin da aka kai a wasu kauyukan yankin tsakiyar kasar. Wannan shi ne taken sharihi jaridar Berliner Zeitfunk. A yanzu dai Najeriya na fuskantar wani sabon tashin hankali, an kashe mutane da dama a kauyen Yelewata na jihar Benue. Wasu majiyoyi sun ce sama da mutane 100, wasu kuma sun ce sama da 200 aka kashe. A cewar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta NEMA, sama da mutane 6,000 ne suka tsere sakamakon harin. Da yawa daga cikin mutanen da suka rasa matsugunansu na bukatar abinci da ruwan sha da magunguna da sauran kayayyakin agaji cikin gaggawa. Iyalai da dama sun rasa komai a cewar Amnesty International, yawancin wadanda suka mutu an konasu har lahira a gidajensu bayan da maharan suka tsare su. An kai harin ne a yankin da ke fama da rikicin kabilanci da addini da tattalin arziki tsawon shekaru. Yankin da wani bincike ya nunar da cewa, a cikin shekaru biyu an halaka mutane 7,000.
Ita kuwa a nata sharhin jaridar Suddeutsch Zeitung na cewa, mulkin cikin shakku da fargaba da tashin hankali a Sudan ta Kudu. Karfin ikon shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir na raguwa, abin da ya sa ake kara shiga fargabar maye gurbinsa. Shin anya ba kasar na fuskantar barazanar wani sabon rikici ba? Rauninsa Salva Kiir ya dade a bayyane, jikin shugaban kasar mai shekaru 73 a duniya da kyar yake iya tsayuwa ba tare da karfasa na karkarwa ba. Yana shan wahalar karanta jawabai, an fara ganin alamun gazawarsa da dadewa. A wani taron koli na Gabashin Afirka a shekarar ta 2023, sai da wani mai taimaka masa ya yi masa kus-kus cikin rada saboda a fili ya gaza gane shugaban kasar Tanzaniya. Jaridar ta ce, lokaci dai ya yi da ya kamata ya sallama mulkin.
A sharhin Jairidar Tageszeitung mai taken: Tabbatacciyar nasarar zabe a Burundi, kujeru kaso 100 cikin 100. Nasarar da jam'iyya mai mulki ta samu a zaben 'yan majalisar dokokin Burundi na fuskantar kakkausar suka daga al'umma, suna ganin an yi magudin zabe. Jam'iyya mai mulki a Burundi CNDD-FDD, ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi a ranar biyar ga watan Yuni da kaso sama da 96 cikin 100 na kuri'un da aka kada. A cewar sakamakon da Hukumar Zabe ta fitar bayan kwanaki shida, babu wata jam'iyya da ta samu kaso biyu cikin 100. Jam'iyya mai mulki za ta rike dukkan kujerun majalisar dokokin kasar, nan da shekaru biyar masu zuwa.