Trump da wasu shugabannin Afirka ta Yamma a jaridun Jamus
July 11, 2025"Baki na musamman a fadar White House" wannan shi ne taken labarin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa a kan ziyarar da wasu shugabannin kasashen Afirka suka kai Amurka a wannan makon mai karewa, kuma da haka ne muke yaye kallabin sharhunan da jaridun na Jamus suka yi a kan Afirka. Ta ci gaba da cewa, Shugaba Donald Trump ya marabci bakin na sa na musamman ciki har da jagoran juyin mulkin, a wajen taron Afirka da aka yi a Washington a ranar Laraba.
Shugabannin kasashen Afirka biyar, daya daga cikinsu wanda ya yi juyin mulki wanda kazalika ya zabi kanshi a matsayin shugaban kasar Gabon. Sai kuma shugaban kasa na biyuda ake wa lakani da shugaban narco saboda zarginsa da kasancewa cikin jiga-jigan kasar Guinea Bissau da suka tsunduma cikin harkar kasuwancin hodar iblis na kasa da kasa. Na uku shi ne dan kishin Afirka da ke son kubutar da kasarsa Senegal daga kangin kasashen Yamma.
Ana iya cewa dai Donald Trump ya gudanar da wani karamin taron Afirka. Taron da akasarinsa ya kasance lokacin cin abincin rana a fadar White House, an shirya shi ne a lokacin kadan kafin farawa. Wanda aka sanar mako guda kafin aiwatar da shi. Zabin kasashen ya kasance abin mamaki. Babu manyan masu fada aji kuma uwa ma bada mama kamar Najeriya ko Habasha. Babu kasashen da ke fama da rikici kamar Sudan ko na yankin Sahel. A maimakon haka, an gayyaci Mauritania da Senegal da Guinea-Bissau da Laberiya da kuma Gabon. Kasashen da ba su da alaka da juna, sai dai suna kan gabar tekun Atlantika.
Ita kuwa jaridar die tageszeitung sharhi ta rubuta mai taken "Sama da mutane 30 ne suka mutu a zanga-zangar da aka yi a Kenya a farkon wannan makon, Shugaba Ruto ya yi barazana ga 'yan adawa".
Jaridar ta ce, zanga-zangar da aka yi a Kenya a ranar litinin ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da yadda aka ruwaito tun da farko. Akalla mutane 31 ne suka mutu sannan wasu fiye da 500 suka samu raunuka, kamar yadda hukumar kare hakkin bil adama ta kasar KNCHR ta sanar a yammacin ranar Talata.
A cewar wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama suka fitar, an kuma kama mutane sama da dubu tare da gurfanar da su a gaban kotu. Yanzu dai wannan ne adadi na karshe bayan da aka tattara tare da tantance dukkan hare-haren da aka kai a fadin kasar.
Sanarwar ta hadin gwiwa ta yi Allah wadai da yadda adadin wadanda suka mutu ya fi yawa a garuruwa da yankuna inda ba zato ba tsammani aka jibge mutane cikin farin kaya da makaman soji domin murkushe masu zanga-zangar. A cewar bayanain, sun rufe fuskokinsu kuma an cire tambarin motocinsu don bad da sahu. A wurare da dama, a baya-bayan nan ma an girke sojoji a kan titunan Kenya wadanda ke yin harbe-harbe kai tsaye. A lokuta da dama, an toshe hanyar da masu ceto za su ceto mutanen da suka ji rauni domin kai su asibiti.
Za mu karkare shirin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta buga labari game da yadda Amurka ke mayar da bakin haure zuwa kasashe na uku. Jaridar ta ce a lokacin yakin neman zabe, Donald Trump ya yi alkawarin korar bakin haure a wani matakin da ba a taba ganin irinsa ba. A wani mataki na aiwatar da wannan manufa, gwamnati na aiki tukuru don tabbatar da cewa karin kasashe na karbar bakin haure daga Amurka.
Ministan harkokin wajen kasar Marco Rubio ya bayyana haka a taron majalisar ministocin kasar da aka yi a lokacin bazara, inda ya ce manufar ita ce aikewa da wasu daga cikin wadanda suka fi kowa aikata laifi zuwa wadannan kasashe. Domin su yi nisa daga Amurka, ta yadda ba za su iya dawowa ba.
A karshen mako, gwamnatin Trump ta ba da rahoton wata nasara ta baya-bayan nan. Ma'aikatar tsaron cikin gida ta sanar da cewa, bayan jinkirin makwanni da alkalan masu fafutuka suka yi, daga karshe an tasa keyar 'yan ci-rani 8 da ake zargi da aikata miyagun laifuka zuwa Sudan ta Kudu. Mataimakiyar sakatariyar tsaron cikin gida Tricia McLaughlin ta ce wadannan masu laifin an fitar da su ne a ranar hutun kasa. Hakan kuma na zama nasara ga bin doka da oda da kare lafiyar Amurkawa.