SiyasaAfirka
Janar Tiani ya karbi rantsuwar wa'adin jagorantar Nijar
March 26, 2025Talla
Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya karbi rantsuwar ci gaba da jagorantar kasar har na tsawon shekaru biyar masu zuwanan gaba, bisa sabon tsarin saita alkiblar kasa.
Karin bayani:Nijar: Kashedi ga malamai kan sukar juna
Da ya ke gabatar da jawabi a yayin bikin rantsuwar a Yamai babban birnin kasar, babban sakataren gwamnatin mulkin sojin kasar Mahamane Roufai, ya ce sabon wa'adin shugabancin na shekaru biyar ya fara ne daga wannan Laraba, kuma an daga likkafar shugaba Tchiani zuwa Janar na soja.
karin bayani:Harin ta'addanci ya halaka mutane 44 a Jamhuriyar Nijar
Da wannan sabon sauyi, yanzu wa'adin Tiani zai kare a shekarar 2030, bayan shafe shekaru bakwai kenan a kan karagar mulkin Nijar.