Rasha ta hana DW aiki a Moscow
February 4, 2022Talla
Manyan tashohi abokan huldar DW kamar ARD, ZDF da Deutschlandradio duk sun yi Allah wadai da matakin Rasha, suna masu cewa hakan ya mayar da 'yancin 'yan jarida ya zama abin tattaunawa.
Shugabar ARD Patricia Schlesinger, Darakta-Janar na ZDF Thomas Bellut da Darakta Janar na Deutschlandradio Stefan Raue sun fada a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa a ranar Alhamis cewa "Ana takaita bayar da rahotanni masu zaman kansu da yawa don fuskantar matsin lamba na siyasa.