Jamusawa na gudun hijira zuwa wasu kasashe saboda rashin aikinyi.
December 27, 2005Yanzu haka dai akwai rahotan karuwan yawan jamusawa kwararru dake ficewa daga cikin kasar zuwa wasu kasashe domin neman ingantacciyar rayuwa.Zainab Mohammab Abubakar na dauke da rahotan dalilansu na ficewa daga kasar zuwa ketare.
Jamusawa masu yawan gasket na ficewa daga wannan kasa,amma bawai don dalilai na talauci da aka sani na gudun hijira a karni na 19 ba,da kuma gudun irin azaban yan Nazi a shekarun 1930,a wannan zamani da ake ciki ,jamusawan na gujewa matsaloli ne da suka dangana da rashin aikin yi.
Jamusawan dai na tafiya wurare masu nisa ne da suka hadar da Amurka da Canada da Australia harda Norway da Netherlands da kuma Austria.Rahotanni dai sun shaidar dacewa a shekara ta 2004 data gabata ,kimanin jamusawa dubu 150 suka tattara yana yanasu suka fice daga kasar,wanda ke zama karo na farko da aka samu samusawa yan sunyi gudun hijira dayawa haka ,tun karshen shekaru 1940s.
Babban dalili da aka danganta da wannan gudun hijira da jamusawan keyi dai shine matakin rashin aikinyi na sama da kashi 20 daga cikin 100 dake addaban sassa sassa daban daban.
Acikin shekaru 15 da gabashi da yammacin jamus suka hade amatsayin kasa guda dai,sama da jamusawa million 1 da dubu dari 8 ne suka bar kasarzuwa gudun hijira.
Karin Manske mai shekaru 45 da haihuwa kuma bajamushiya wadda ta koma kasar Amurka da zama da yayanta biyu ,shekaru 8 da suka gabata ,tace abun takaici hali na rashin aikinyi daya tsamari a Jamus.
Datake hira da kamfanin dillancin labaru na reuters a birnin Los Angeles,tace abun abun takaici ne kasancewar jamusawa mutane ne masu fasaha,tace bata muradin komawa Jamus domin ita mutun ce mai son cigaba akan duk wata fasaha data kirkiro koda na gyaran takalmi ne,kuma zatayi nasara akansa.
Aynzu haka dai an kiyasta cewa akwai kimanin jamusawa dubu 70 dake da zama a kudancin California dake Amurka,wadanda mafi yawansu ayan shekarun nan ne suka kaura zuwa can da zama.
A baya can dai jamusawa da sukayi gudun hijira saboda yan Nazi,sun koma Hollywood ne da zama,kana bayan yake yaken duniya jamusawa da dama suka maye guraben aiki a wasu kananan garuruwa dake Amurkan.
Rahotan daya fito daga maaikatar kididdiga ta Jamus dake Wiesbaden ,na nuni dacewa jamusawa kimanin dubu 150 da 667 da suka fice daga kasar a bara zuwa kasa wasu kasashe 200,jamusawan dubu 12 da 976 ne suka koma Anurka,sai kuma Swirzerland 12,818 kana wasu dubu 8,532 suka je Austri,ayayinda Britania ta karbi bakuncin jamusawa dubu 7,842.
Wasu kasashe da sukayi maraba da wadanan yan gudun hijira jamusawa sun hadar da faransa da Spain da Holland da kuma Belgium.
To sai dai manazarta sun bayyana cewa wannan adadi na hukuma ne kadai,domin adadin jamusawa dake tserewa daga matsalolin rayuwar jamus sunfi yawan wadanda aka sanar.