SiyasaJamus
Jamus za ta fara shari'ar masu yi wa Rasha leken asiri
May 20, 2025Talla
A wannan Talata, babbar kotun birnin Munich a nan Jamus za ta fara sauraron shari'ar wasu mutane uku da ake zargi da yi wa Rasha leken asiri, da yi wa Jamus makarkashiya a cikin tsarin aikin sojinta da kuma sufurin jiragen kasa. Mutane ukun dai suna cikin dakarun da Rasha ta yi amfani da su wajen yakar Ukraine a matsayin sojin gona, inda aka kama biyu daga cikinsu a jihar Bavaria bayan wani samame da 'yan sandan Jamus suka kai maboyarsu.
Karin bayani:Jamus: Scholz ya soki Trump kan kotun ICC
Ko a makon da ya gabata ma an kama wasu 'yan kasar Ukraine uku a nan Jamus da kuma Switzerland da ake zargin cewa Rasha ce ta turo su nan Jamus don kulla wani makirci da kutunguila.